Labarai
HISBAH a Kano ta haramta yada hotunan Zahra Bayero AmaryarYusuf Buhari
Hukumar HISBAH dake Kano ta haramta yada hotunan Amaryar dan Shugaban kasa, Yusuf Buhari, watau Zahara Ado Bayero.
Hotunan Zahra sun yadu sosai a shafukan sada zumunta inda suka jawo cece-kuce, an rika caccakar HISBAH ta Kano da cewa, da ‘ya’yan talakawane da an kamasu.
Kamar yadda hutudole na ruwaito.Saidai sabbin Rahotanni dake Fitowa daga Kano na cewa, HISBAH ta haramta yada hotunan Zahra wadda diyace ga sarkin Bichi, inda ta bayyana cewa, yin hakan Haramunne.
Kwamandan HISBAH, Haruna Ibn Sina ne ya bayyana haka inda yace masu yada hotunan diyar Zahra sun aikata laifi kuma itama bata fi kargin hukuma ba, inda ya bayyana ta da cewa abinda ta aikata ba ya kan koyarwar Addinin Islama.