Labarai

Harin NDA zai sa mu hanzarta kawo ƙarshen ‘yan fashin daji – Buhari

Shugban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce harin da ‘yan fashin daji suka kai Kwalejin Horon Sojoji ta NDA zai sa gwamnatinsa “ta hanzarta ɗaukar mataki maimakon sanyaya mata gwiwa”.

Bbchausa ta ruwaito. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Femi Adesina ya fitar, Buhari ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan sojoji biyu da maharan suka kashe ranar Litinin da tsakar dare, yana mai cewa “ba za su rasu a banza ba”.

Wasu rahotanni na cewa maharan sun kutsa makarantar ta horar da sojojin Najeriya na ruwa da na ƙasa da na sama a birnin Kaduna bayan sun yi shigar sojoji. Sai dai hukumar kwalejin ta ce sun haura ne ta katangar da ke kewaye da makarantar.

Harin NDA zai sa mu hanzarta kawo ƙarshen 'yan fashin daji - Buhari
Harin NDA zai sa mu hanzarta kawo ƙarshen ‘yan fashin daji – Buhari
Hoto:facebook
Daga :bbchausa

“Ganin cewa harin na zuwa ne a lokacin da sojoji suka matsa wa ‘yan fashi da masu garkuwa da mutane da sauran masu laifi, shugaban ƙasa ya ce wannan mummunan aikin zai jawo hanzarta kawo ƙarshen rashin imani kwakwata kuma abin da sojoji ke yunƙurin cimmawa kenan cikin ƙanƙanin lokaci,” a cewar sanarwar.

Sanarwar da ya fitar ranar Laraba ta ƙara da cewa “maimakon hakan ya sanyaya gwiwar dakarunmu kamar yadda aka tsara, zai ƙara musu azama ne wajen kawo ƙarshen miyagu a ƙasar nan, a cewar Buhari”.

Wani hoto da ya karaɗe shafukan zumunta na nuna gawar sojan da ‘yan bindigar suka sace a harin amma BBC ba ta iya tantance gaskiyar lamarin ba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA