Hausa Series FimKannywood

Gwamnatin Kano za ta taka wa Tijjani Asase burki a kan diramar ‘A Duniya’

GWAMNATIN Jihar Kano ta ƙudiri aniyar kawo gyara a labarin da ake gabatarwa a cikin fim ɗin nan mai dogon zango na ‘A Duniya’ wanda fitaccen jarumi Tijjani Abdullahi (Asase) ya ke haskawa a YouTube.
Mujallar Fim ta ruwaito cewa ofishin mai bai wa gwamnan Kano shawara kan harkokin makarantun tsangaya, Sharif Ahmadu Sha’aibu, ya fitar da wata sanarwa a yau Laraba inda ya ce sun yanke hukuncin ɗaukar matakin ne saboda wani ƙorafi da wasu su ka shigar a kan fim ɗin.
A cikin wata takardar sanarwa da mujallar ta samu, ofishin ya ce a taƙaice, “A sakamakon takardar da aka rubuta wa wannan ofishi mai albarka ta ƙorafi a kan shirin fim mai dogon zango ‘A Duniya’ mai dogon zango na kamfanin Brainscope, takardar mai kwanan wata 1/1/1443 9/08/2023, domin haka na ke rubuta wannan takarda don sheda wa al’uma da Gamayya mun karɓi saƙon takardar ƙorafi a kan wani sashe daga wannan fim. Gwamnati za ta yi umarni wajen kawo gyara a cikin wannan fim ‘A Duniya’.

Takardar sanarwar da gwamnatin Kano ta bayar a kan shirin ‘A Duniya’. A hoton farko, fostar diramar ne mai nuna wasu jaruman shirin, cikin su har da Tijjani Asase

“Mu na fatan za a ci gaba da ba wa gwamnatin Jihar Kano goyon baya da addu’a wajen cigaban addinin Musulunci da harkokin ilimi free education da makarantun mu na tsangaya masu albarka, da samar da tsaro a Jihar Kano baki ɗaya.
“Daga ƙarshe, mu na yi muku fatan alheri. Allah ya ba mu albarkar Ƙur’ani mai girma, amin. Mun gode.”
Sai dai ofishin bai faɗi takamaiman ƙorafin da aka gabatar masa ba da kuma irin matakin da zai ɗauka.
‘A Duniya’ dai shiri ne da ake nunawa a wata tashar YouTube mai suna Zinariya wadda ta ke mallakin Asase.
Shirin ya na nuna wasu daga cikin halayyar son zuciya da matasa su ke nunawa ta hanyar mutuwar zuciya tare da yin sace-sace wanda har ta kai su ga da-na-sanin rayuwa.
Idan kun tuna, mujallar Fim ta taɓa kawo wani rahoto na yadda wasu masu kallo a Kano su ka yi kukan cewa fim ɗin ya na ɓata tarbiyya ta hanyar koyar da muggan ɗabi’u ga matasa da su ka haɗa da tallata harkar daba da ƙwacen wayar hannu.
A lokacin, an yi raɗe-raɗin cewa wai har hukumomin tsaro sun dakatar da nuna fim ɗin.
Sai dai a labarin da mu ka wallafa, Asase ya ƙaryata zargin da ake yi wa fim ɗin, ya ce kawai ana yi masa hassada ne tare da rashin son ganin cigaban sa da wasu ke yi.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button