Labarai

BINCIKE: Nan gaba kaɗan maza zasu rasa matan da za su aura saboda ƙarancin mata a duniya

Rahoton ya ce Najeriya da Pakistan na daga cikin ƙasashen da nan gaba maza za su iya fin mata yawa, amma abin zai yi sauƙi bayan shekara 20 masu zuwa.
Bincike ya nuna nan gaba maza za su rasa matan da zasu aura saboda ƙarancin mata a duniya.
Kamar ydda shafin dokinkarfe na ruwaito Wannan na zuwa ne bayan gudanar da wani bincike kan ƙasashe 204 a faɗin duniya baki ɗaya.
Rahoton ya bayyana irin matsalar da maza za su shiga matuƙar ba a nemi mafita kan wannan ba.
Wani bincike kan alkaluman jinsi a duniya ya gano cewa wasu matakai da mutane ke ɗauka a kan haihuwa za su kawo ƙarancin mata a duniya a nan gaba.
Rahoton binciken da cibiyar lafiya ta BMJ Global Health ta gudanar kan bambanci tsakanin jinshi, ya nuna son haihuwar ƴaƴa maza da kuma al’adar kyamar haihuwar mata sun sa ana yawan zubar da cikin ƴaƴa mata ko kashe jarirai mata a wasu ƙasashe.
Binciken da cibiyar ta gudanar a wasu ƙasashe 204 ya nuna daga shekarar 1979 zuwa 2017 an kashe jarirai mata ko an zubar da cikinsu sau miliyan 45.
Sakamakon binciken ya ce a shekarar 1970 da ƴan kai, jarirai maza da aka haifa a Kudancin Turai da Asiya sun fi mata, ƙasashen Indiya da Pakistan kuma ke da kashi na 95 cikin 100 na jarirai mata da aka zubar da cikinsu ko ake kashewa.
Marbucin rahoton, Dokta Fengqing Chao, ya ce a halin yanzu, maza na fama da ƙarancin matan da za su aura a wasu daga cikin ƙasashen da abin ya shafa.
Rahoton ya ce Najeriya da Pakistan na daga cikin ƙasashen da nan gaba maza za su iya fin mata yawa, amma abin zai yi sauƙi bayan shekara 20 masu zuwa.
Dokta Chao ya ce daga yanzu zuwa shekarar 2030 akwai yiwuwar rasa jarirai mata 4.7 kuma illar ta wuce batun rashin samun matar aure.
Ya ci gaba da cewa idan ba a yi wa tufkar hanci ba, nan gaba a cikin ko wadanne maza uku, mutum daya ne zai samu matar da zai aura.
Akwai bukatar yin dokoki da za su tabbatar da daidaiton jinsi domin magance karancin abokan aure.
Ƙarancin mata a cikin al’umma na iya haifar da miyagun dabi’u da tashin hankali da kuma kawo cikas a zamantakewar al’umma.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button