Wani Ɗan Siyasa ya Ɗauki Nauyin kula da Lafiyar Jarumi Sani Garba SK
Masha Allah wani bawan Allah dan siyasa ya dauki nauyin kula da rashin lafiyar jarumin masana’antar kannywood wanda majiyarmu ta samu zuma times sun ruwaito wannan labari.
Inda sunka wallafa a shafinsu na sada zumunta.
“Sanannen ɗan wasan ƙwaikwayon nan Sani SK da yajima yana fama da jinya yasamu wani ɗan Siyasa da ya ƙuduri aniyar taimaka masa ta hanyar ɗaukar nauyin kulawa da Lafiyar shi.
Malam Inuwa waya wanda ake kira da (RABA GARDAMA) shine ya dauki nauyin kula da rashin lafiyar da Sani SK dan dago ya dade yana fama da ita.
An bayyana cewa tun bayan Jin rashin lafiyar da SK yake fama da ita tasa Malam Inuwa Waya takanas ta Kano yayi tattaki har gidan Sani SK Dan dago inda ya duba shi kuma yayi masa Ikhsanin Alkhairi kuma nan take ya ɗauki nauyin kulawa da lafiyarsa ba tare da wani bata lokaciba, jin dadin hakane tasa yan unguwa da shuwagabannin yan wasan hausa da abokanai suka yi ta godiya da nuna jin dadin su akan hakan tareda fatan Alkhairi.
Sai muce Allah ya bada lafiya yasa kaffara ne Amin.”