Labarin Wani Hariji Ɗan Ƙasar Zambiya Mai Mata 47, Yana kwanciya Da 10 Kullum, Yana Da ƳAƳA 520 JIKOKI 1,200
Yau labarin wani harijin mutum ɗan ƙasar Zambiya muka kawo muku, hakika a labarin nan nasa akwai abin mamaki da al’ajabi ƙwarai.
Wannan mutumi da kuke gani a hoto dan ƙabilar Tonga ne, ya auri mata guda 47, kullum yana kwanciya da guda goma daga cikinsu, kuma ya biya musu bukata har su gamsu.
Yana da wata ƙararrawa a dakinsa, wacce yake kaɗa wa domin wacce ya gama biyawa buƙata ta fita, wacce ke bin bayanta sai ta shigo daga ciki.
Sauran matan nasa suna jiran layi, yayin da zai biyawa wacce ta shiga daga ciki buƙata, ya kaɗa ƙararrawa wata ta shiga.
Ƙarin wani abin mamaki shine, duk matan nasa goma cikin daren suke komawa gidansu zuciyarsu warkan, domin harijin mijinsu ya biya musu bukatarsu.
A ƙarshe mutumin dan kabilar Tonga mai shekaru 60, ya haifi ƴa ƴa masu suna yaya har guda 520, kuma yana da jikoki aƙalla guda 1, 200.
Yanzu haka wannan mutum ya riga mu gidan gaskiya. Ya rasu yana da shekaru 60 a duniya.