Labarai

Innalillahi Wa Innaa Ilahin Ra’juun : Jaridar sahara reporters ta wallafa Labarin Batanci mai dauke da kaskantar da darajar Annabi Muhammad (s.a.w)

Jaridar Sahara Reporters mallakin Sowore ta wallafa labarin batanci mai dauke da kaskantar da darajar Annabi Muhammad (SAW)
Sahara Report sunce sakataren yada labarai na kungiyar yarbawa Afenifere Jare Ajayi yace Sunday Igboho yana kamar matsayin Annabi Muhammad (SAW) yake, wanda ya tsere daga Makkah zuwa Madina saboda cutarwan da aka masa
Wannan cin zarafi ne da batanci wa shugaban mu Annabi Muhammad (SAW), ya za’a hada boka matsafi irin Sunday Igboho wanda ba Musulmi ba ace wai yana kama da Annabi Muhammad (SAW)?
Idan kwatance zasu kawo da Annabi me ya hanasu kawo kwatance da Annabi Musa (Prophet Moses) tunda ya zo a cikin Bible din da su Sunday Igboho sukayi imani dashi kuma shima Annabi Musa zaluncin Fir’auna ya sa ya tsere daga gari tare da ‘yan uwansa Yahudawa?
Billahi wannan abin da niyya sukayi, sun ambaci Annabi Muhammad (SAW) da manufar kaskantar da daraja da batanci gareshi saboda su harzuka Musulmai
Muna kira ga hukumar kula da harkokin watsa labarai a Nigeria NBC ta dauki mataki kan wannan batanci da Sahara Reporters ta wallafa akan Annabin mu
Sahara Reporters tun suna yiwa manyan Malaman addininin mu na Musulunci batanci ana kyalewa yau batancin nasu ya hauro kan Manzon Allah Annabi (SAW), jama’ar Musulmi menene amfanin rayuwarmu idan ba za’a tsaya a dauki mataki ba?
Muna kira ga Gwamnatin Nigeria ta gaggauta daukar mataki akan batancin da jaridar Sowore ta wallafa akan Annabin mu
Muna kira ga duk wani Malami mai fada aji a kasarnan, da duk wani shugaban Musulmin tun daga kan mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Abubakar III har zuwa na Kasa su dauki mataki bisa dokar kasa akan batancin da jaridar Sahara Reporters ta yiwa Annabin mu
‘Yan uwa Musulmi kowa ya isar da wannan sakon ta sigar da ta dace har sai an dauki mataki, Wallahi ba zamu yadda ba.
Daga Datti assalafy

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button