Kannywood

Hausawa Ko Turawa? Yanzu saboda Allah waɗannan ‘yanmatan sun yi kama da mawaƙan Hausa!?

Ko dai su mawaƙan da daraktocin da su ke bai wa waɗannan ‘yanmatan irin waɗannan suturun da sunan waƙar Hausa ba su da mafaɗa ne? Ko dai su na da wata manufa ne?
Abu wasa wasa sai daɗa haɓaka ya ke. In su na son su waƙoƙin Turanci, su nemo Turawa su yi musu rawa; ba wanda ya ce kar su yi, amma akwai wulaƙanci da rainin hankali a cusa yarinya a cikin tsukakkun kaya a sa ta rawa da su, wai kuma waƙar Hausa, kowa kuma ya zuba ido ya na kallo.
A duk lokacin fa da mutum ya rasa al’adar sa, to ya rasa ta, an gama cin sa da yaƙi, ya zama hoto.
Ya kamata waɗannan mawaƙa su yi wa kan su faɗa. Ba abin da zai hana su bai wa waɗannan ‘yanmatan kayan Hausawa su sa in ya zama dole sai sun yi rawa da waƙa da su.
Ba wani burgewa ba ne a sa kayan Turawa. Mayar da kai baya ne. Saboda ko Turai ka je da kayan ka na gida sai ka fi burge su, sai ka ga su na tsayawa su na ma magana. Amma ka sa nasu ko kallo ba ka ishe su ba.
Shi ya sa da na ga su Rahma Sadau wai an je Amerika an sa ƙananan kaya har da ƙona gashi na ce kash!, waɗannan sun kwafsa. Allah Ya kyauta.”
Daga Dr. Maryam Ali Ali,
Sa’adatu Rimi College of Education, Kano

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button