Labarai
Gwamnatin Kano bata aminta da tuban Abduljabar ba
Advertisment
Kwamishinan kula da harkokin Addinai a jihar Kano Dakta Muhammad Tahar Adam (Baba Impossible) ya shaidawa manema labarai a yammacin ranar Litinin cewar Gwamnatin Kano sam bataa karbi tuban da Malam Abduljabar ba.
A cewar Kwamishinan, Malam Abduljabar bai janye bai tuba ba, domin janye kalamai ba tuba bane, ya bayyana sharadan tuba wanda yace sai an bisu ne tuba yake tabbata.
Baba Impossible ya bayyana cewar Gwamnatin Kano zata cigaba da aniyarta ta daukar matakin da ya dace kan Abduljabar.jaridar nigeriandaily na ruwaito.