Fitacciyar Jaruma Rachael Oniga ta Rasu
Dan ta mai suna Olatunji ne, ya tabbatar wa manema labarai mutuwar ta, a yau Asabar.
Acewar shi, mahaifiyar ta shi, ta mutu ne da musalin karfe goma na daren jiya juma’a.
Kafin mutuwar Margayiya Oniga, ta sha fito a ciki wasu fina-finai masu, a Masana’antar Nollywood na turanci, da kuma na kabilar Yarbawa.
An haife ta ne a ranar 23 ga watan Mayun shekarar 1957, inda ta fara fito wa a matsayin Jaruma a shekarar 1993, da ta fito a cikin fim Mai sunan Blockbuster da kuma Onowe da aka yi shi da yaran Yarbanci.
Tsohuwar jarumar Mai shekarar 64, ta yi aiki da wani kamfanin Injiniyancin na kasar Habasha, dake da Babban ofishi a Nigeria.
A wani hira da aka yi da ita kafin rasuwar ta ta ce, ta dai-na aiki da kamfanin bayan tayi aure domin tafara tara iyali, sai dai auren na ta bai jima ba, ta fito.
Bayan rabuwar ta da mijin ya’yan na ta, sai kuma ta koma taka rawa a Masana’antar fina-finai na Nollywood.
Kazalika ta sha fadi a tattaunawar ta da mane ma labarai kafin rasuwarna ta cewa, babban danasani da ta yi a rayu shine, rashin tsawa na neman hakkin ta na aure, bayan rabuwar ta, da mijin na ta.