Kannywood

Datti Assalafy Ya munana Zato Kan Rashin Lafiyar Maryam Yahaya

A yau din nan shahararren marubucin nan datti assalafy yayi rubutu akan rashin lafiya jaruma Maryam Yahaya da ta kwashe wata ukku tana jinya wanda a rubutun nasa akwai chakwakiya inda wasu na gasgata shi, wasu na Qalubalance shi, wasu kuma na danganta laifin ga ita yarinyar da iyayenta.
Ga Abinda ya Wallafa a shafinsa na sada zumunta.
KIRA ZUWA GA KUNGIYOYIN KARE HAKKIN MATA NA DUNIYA
Jaruma a masana’antar Hausa film Maryam Yahaya karamar yarinya ce, kafin shigarta Hausa film tana tallen kayan koli anan unguwarsu a birnin Kano, tana kuma soya awara a kofar gidansu, suna rufawa kansu asiri da iyayenta, wanda suke masu karamin karfi ne, wato talakawa abin tausayi
Lokacin da aka shigar da yarinyar nan wasan hausa film tudun kirjinta bai gama girma ba, ma’ana bata gama zama cikakkiyar balagaggiya ba, da mutuncinta da komai, da farko Mahaifinta bai so ba, yaudaransa akayi aka jefa ‘yarsa wasan kwaikwayo
Abokan sana’arta bayan sun ruguza mata rayuwa, sun kawota gidan iyayenta sun jibge a gida, yanzu ko ziyara duba halin da take ciki basa yi, sun kyamaceta
Wannan cin zarafi ne da keta hakkin rayuwar mata dangin rauni, ba a haka ‘yan Hausa film suka dauketa a gidan Mahaifinta ba, Mahaifinta bai da karfin daukar Lauyoyin da zasu kwata mata ‘yanci a biyata diyya, tunda sun kashe mata rayuwa
Muna kira ga hukumomin Gwamnati da manyan kungiyoyin kare hakkin yara mata su kawo dauki wa Maryam Yahaya, a taimaka wajen kwato mata hakkinta da na iyayenta
Muna izna ga sauran ‘yan mata da suke sha’awar wasan kwaikwayo, ku gaji Hausa film babu alheri a ciki ko kadan, sai da na sani marar amfani
Yaa Allah Ka bawa Maryam Yahya lafiya, Ka yafe mata, Ka bada ikon kwato mata hakkinta Amin”.
Wanda fiye da mutum dubu ne nayi masa martani amma ga kadan daga ciki.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

4 Comments

  1. Wannan gayen bayada Aikin yine Wai a kwato Mata yancinta awaken wa kenan awajen Wanda ya Dora Mata rashin lafiyae ko awajen iyayenta ko Kuma a wajen Ali nuhu ko qungiyar shirya Fina finai Kajifa Dan Allah magana mara ma.ana Maryam ai na yarinya bace 20 something ai yawuce ace anci zarafinta in Banda qiyayya da wannan masana.antar kawai anbi ansawa Kannywood ido tin kafin Kannywood sufara film ake kallon film Wanda yake nuna abubuwan da Bai kamata ace bahaushe yagani ba ballantana yayi koyi Amma film din Hausa bazaga an rungumi mace ko an simbaceta ba Amma sauran finanai da ake kallo na turai har kusanta akeyi aciki Amma bantabajin wani yace Yana Bata tarbiyya ba sai Hausa film shikadai aka sawa ido idan kaga mutum yayi Abu na marasa tarbiyya Daman can baida ita ne Hausa film bazai iya Bata tarbiyya ba idan har akwaita Duk masu cewa Hausa film na Bata tarbiyya to nidai kallon da nake Masa shine Mai hassada da qin nashi Wanda wannan Daman halin Bahaushe ne qin nashi Allah yasa mudace

    1. Ya Allah ka iyamana bunda bazamu iyaba Allah kakare musulunci da musulmai ka tausaya mana ya Allah kashir yamu ka yaye mana talauci da bakin cikin duniya da lahira yahaiyu ya qayyum.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button