Labarai

Cikakken Bayyani Game Da Wanda Yayi Ɓatanci Ga Manzon Allah (Saw) A Sokoto

Alhamdulillahi wannan shine labarin da dan gwagwarmaya addinin musulunci malam Jamilu Sani Rarah yayi game da yadda alamarin ya faru da yadda anka sha fama wajen kama wannan zandiki ga bayyanin nasa kamar haka.
Wannan shine bayanin da nayiwa wasu ‘yan uwa da suka tareni suka bukaci jin wani Abu daga bakina, Ganin cewa, mune farkon wayanda suka fara Neman wannan Yaron kuma mune mukayi nasarar cafkeshi.
Farko Duk zafin kan da ‘yan uwa suke ji da kishin da Suke ji hakika Muma wallahi muna Jinsa domin Hatta a Lokacin da muke kan nemansa Wallahi tallahi nayi Kuka saboda konani da abin yakeyi a zuciya.
Sunce, Bai kamata a Tsaya bincike ba, nace wannan kuma Kuskurene Babba domin Ni dasu duka muna yin Facebook kuma dukan mu babu mai tabbacin cewa, Gobe ko Jibi ba za’a Iya Yin hacking din account dinsa ba yana cen yana bacci ayi masa irin wannan aika aikar ba. Don haka a addinance bincike ne mataki kafin hukunci.
Munje Neman Yaron gidansu da kyar muna samu gane gidan, bayan mun gano Sai ‘yan Uwan Yaron Suka ce mana wallahi bashi da Hankali tare da nuna mana cewa, ai ya saba yin irin wannan mummunan rubutun a jikin ginin gidan nasu suna gogewa (hakan yasa suka jani suka nuna min na gani da idona).
Kai tsaye Sai muka bukaci su bamu Yaron Sai sukace, ai tunda baida Hankali sun turashi Assibitin kware anan mukayi waya da Comrd Husaini Muhammad, Comrd ya bada Gudumuwa sosai wajen tabbatarda baya Asibitin kware Ashe wasu daga cikin ‘yan Uwan Yaron ne suka turashi wani gari ba Asibitin kware ba.
Anan Comrd Husaini ya Bincika mana Kware Sai ya tabbatar mana da Ashe baya kware sun turashi wani wurine, anan muka tsoratardasu akan aikata haka da sukayi tare da nuna musu ai su kawoshi shine mafita garesu ko dukansu su samu matsala. Nan ne suka Fahimcemu tare da Kawo wannan Zindikin Yaron.

Zindikin Yaron kenan

Daga Kawosa Wallahi Na Fahimci Lalle bsshida Lafiya, Domin yawan Sumar da ke Kansa da Dattin da ke cikin kumbarsa kawai sun Isa ka tabbatarda mahaukaci ne a gabanka.
Nan muka daukeshi muka kaishi state CID tare da Hannunta shi garesu.
Wannan shine hoton zindikin wajen state CID Office

Akwai abinda Bai kamata In fada a Facebook ba, Amma kuma Ya zama dole In fada domin Al’umma Susan cewa, ‘yan Sanda ma Masoyane na Annabi (Saww).
Team dinda muka je nemansa Dasu na ‘yan Sanda team ne na ‘yan Sandan da Duk Fading Jahar Sokoto ana tsoronsu.
Wallahi abinda muka Shirya da Munga Yana da Hankali da Yanzu wani labarin akeyi ba wannan ba.
A yanayin bashi da lafiya da damuwa yadda ya koma hoto: Facebook

Kuma Na Tuntubi wani daga Cikin Manyan malaman mu na Gaya masa halin da muka ga wannan zindiki ( eh zindiki tunda in ko Jjnjiri ya zagi Annabi wallahi bazan tausaya masa ba balle had in kirashi da wani suna daban). Wannan Malamin Ya bada Shwara mai Kyau game da shi kuma In shaa Allahu Idan Aka bita duka Zamu fahimci tabbas an Kate martabar Annabin mu Abin Alfaharinmu.

Malamin yace Yayi a yi binciken kwakwaf na kwakwalwarsa domin tabbatarda da abinda ake cewa na rashin hankalinsa koda kuwa Siffa da Surarsa Sun Bada baida hankali

Hakika Matasanmu sun Nuna Kishin su sosai ga Abin Alfaharinmu tare da burgeni Matuka tabbas Sokoto tana nan da sunanta Birnin Shehu.
Jinjina Ga Su, Prof. Mansur Sokoto Malam Bello Hasaan Almustapha, Sirajo Abdullahi, Dan Almajiri, Zubairu Abdullahi, Engr Bello Rabah, Comrd Husaini, Shattiman Goronyo, Zannan Goronyo, Zannan Rabah, Abbas Kwarare, Malam Imran Dasauransu hakika ‘yan Uwa Kun nuna Kokari kwarai da gaske.
Jamilu Sani Rarah Sokoto
Fri 09-07-2021″

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button