Bidiyo : Prof. Ibrahim Maqari Yajenye Kalamansa Kuma Yabada Hakuri Ga Malaman Izala Da Salafiyya
ALHAMDULILLAH
Sheikh Professor Ibrahim Maqari (H) ya fito ya bada hakuri wa dukkan ‘yan uwa Musulmai daga kowace irin akida da kungiya ta addinin Musulunci a Nigeria wadanda suka bayyana bacin ransu tare da yin raddi gareshi sakamakon maganar da yayi akan shugaban Zindikai na jihar Kano wakilin ‘yan shi’ah Abduljabbar
Professor Maqari ya nesanta kansa da akidar Abduljabbar, sannan ya amince da kuskurensa ga duk wanda yake ganin yayi kuskure, kuma ya bada hakuri wa kowa, daga karshen jawabinsa ya roki ‘yan uwa Musulmai da a shagalta akan lamarin addini, ayi watsi da sukar juna
Professor Maqari ya burgeni matuka, Malaman da suka masa raddi ba tare da zagi da cin zarafi ba suma sun burgeni, ‘yan zafin kai da suka hada da zagi da cin mutunci a raddinsu basu kyauta ba, sai su dauki darasi anan
Mun fada muka Sheikh Professor Ibrahim Maqari mutumin kirki ne, yana da saukin kai da kuma gudun duniya, kuskure yayi inda yayi magana akan wanda bai sani ba, a rayuwa babu wani mutum da yafi karfin yayi kuskure da tuntuben harce
Muna rokon Allah Ya kara hada kan Musulmai a tafarkin gaskiya Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.
Ga bidiyon nan kasa sai ku saurara.
https://youtu.be/0MoG_JSJ5RA