Addini

Bidiyo : Na gwammace in kurumce ko in mace ma da in Saurari Abin da Abduljabar Ke fadi – Inji Prof maqarfi

Da Farko shehi yayi jan hankali akan baudadden tunani akan al’amura wanda da an fada maka wani abu zaka fara wani tunanin na dabam musamman wanda yake ba mai kyau ba, Prof, yayi jan hankali akan wannan, wanda har ya bada misali inda yace da an ambaci Katsina abinda yake tunawa shine Bishiyar delbejiya da kuma zafin Rana, Maulana Prof yace basuda alaqa a Luga ammah shi yake fara tunanowa,
Maulana sai yayi shimfida tare da zaburarwa kaji a ranka da an kira Annabi (S.A.W) abinda zaka fara tunawa shine, hakurinsa, adalcinsa, tausayinsa, da sauran abubuwa na jinkai tare da Sayyiduna Rasulullahi (S.A.W)
Gaba ta gaba Prof yaja hankali akan malaman da basa daukar karatu a gaba malamai kamar dai yadda Malam mai gaba gadi yake koyi da kanka kace ka gane…
Maulana Prof ya gargadi masu tsayawa suna sauraran irin wannan mahaukata dauke da rigar malunta, Maulana Prof yayi anfani da kalmar shaqiyi, wawa mahaukaci don lamarin Malam gaba gadi yafi kama da haukar…
Maulan Prof yaja hanjalin al’umma masu yada irin barnan dan tamore a bayan kasa sannan su tsohe kunnuwansu da jin irin shurbucin da Malam gaba gadi yake yi a cikin irin wannan karantarwa…
Prof yayi kira ga malamai masu kokarin sanya Siyasa a cikin lamarin waqi’ar Dan Tamore saboda wani qullalliya dake tsakaninsu, inda yayi kira da a nufi zatin Allah…
Sai dai na lura tabbas Prof kamar yadda yace bayason magana akai sbd bai saurara ba, tabbas na yarda don da ace Maulana Prof ya taba saurara dan tamore inada yaqini da doka tana hanunsa da yanzu wannan batamore ya dade hukuntashi, sbd sanin irin soyayyar da Prof ke yiwa Sayyiduna Rasulullahi (S.A.W)..
Allah yasa mu dace ya mana tsari da irin wannan mummunan zamiya. Amiin
Daga: Yusuf Adamu Abdullahi
Ga bidiyon nan kasa sai ku saurari daga bakinsa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button