Kannywood

Allah Ne Ya Dorawa Maryam Yahaya Rashin Lafiya Ba Yan Kannywood Ba – Afakallah

Biyo bayan bayyanar labarin halin rashin lafiya da fitacciyar jarumar fina-finan Hausa ta Kannywood Maryam Yahya ta ke ciki, jaridar Dokin Ƙarfe TV mun tattauna da shugaban hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano, Mallam Isma’ila Na Abba Afakallah musamman akan zarge-zargen da ake yi wa masana’antar ta Kannywood da yin watsi da jarumar a wannan hali na rashin lafiya mai tsanani da ta ke ciki.
Shugaban hukumar tace fina-finan ya bayyana cewa ba gaskiya ba ne cewa wai masana’antar ta yi watsi da jarumar domin a kullum a akwai ɗumbin jarumai da su ke tururuwar zuwa duba jarumar domin jajanta mata da yi mata addu’ar samun sauƙi wurin Allah.
Daɗi da ƙari, “Mu na so jama’a su gane cewa, Allah shi ne ya ɗorawa Maryam Yahya wannan rashin lafiya ba ƴan Kannywood ba kamar yadda ya ke ɗorawa kowane bawa rashin lafiya a duk lokacin da ya so ba tare da duban matsayinsa ba. Akwai manyan mutane waɗanda Allah Ya jarabce su da jinya, wasu jarumai ne wasu ƴan siyasa, wasu ƴan kasuwa da malamai da manyan sarakuna. Wasu sun mutu, wasu sun warke, wannan duk nufi ne na Allah, mu yi wa Maryam addu’ar samun sauƙi ba cece-ku-ce ba”. Cewar Abba Na Afakallah.
Dangane da yaddda sauran jaruman masana’antar su ka ɗauki jarumar kuwa, Isma’ila Na Abba ya shaida cewa ko da a lokacin da aka gabatar da addu’ar ukku ta Marigayiya Hajiya Zainab Booth jaruman masana’antar gabaɗaya sun ɗunguma manya da yara mata da maza da shugabanni duka an je an ƙara duba halin da take ciki.

Shugaban hukumar tace fina finai Ismail Na abba Afakallah

Haka zalika, “Baya da wannan Maryam Yahaya jaruma ce mai ladabi da biyayya ta na da muhimmanci a masana’antar Kannyood, masana’antar ta taimaka mata ta gina kanta ta samu kuɗaɗe ta mallaki gida nata na kanta, ta mallaki duk wani abin buƙatar rayuwar ɗan adam a sanadiyyar wannan masana’anta ba wai talaka ba ce. Sannan ita ma ta kawo gudunmawa mai girma ga cigaban masana’antar ta na kuma mutuntawa da girmama kowa a wannan masana’anta, ana zaman lafiya da ita, saboda haka ita ɗin ba a bar watsi ba ce kamar yadda wasu su ke zargi, ana zuwa duba ta tare da ba ta duk wata kulawa gwargwadon iko, muhimmin abu shi ne mu cigaba da nema mata sauƙi wurin Allah”. Inji Isma’ila Na Abba Afakalla shugaban hukumar tace fina-finai na Jihar Kano.
DAGA Jaridar Dokin Ƙarfe TV

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA