Aamir Khan ya saki matarsa bayan shekaru 15 suna tare
Fitaccen jarumin fina-finan Indiya, Aamir Khan ya sanar da rabuwa da matarsa Kiran Rao da suka shafe shekara 15 tare matsayin miji da mata.
Ma’auratan sun bayyana dalilin rabuwarsu cikin wata sanarwa da suka fitar inda suka ce da yardar juna suka rabu amma sun amince su kula da yaronsu tare da kuma ci gaba da ayyukansu.Kamar yadda gidan jaridar bbchausa na ruwaito.
“A cikin waɗannan shekaru 15 masu dadi da muka yi a tare mun yi rayuwa cikin farin ciki da jin dadi, kuma soyayyarmu ta bunƙasa ne kawai cikin aminci, girmamawa da kauna,” in ji su.
“Amma yanzu muna son mu buɗe sabon babi a rayuwarmu – ba matsayin mata da miji ba, amma a matsayin iyaye da kuma ƴan uwan juna.”
Khan da Rao sun fara haɗuwa ne lokacin da suke yin wani fim a 2001 inda Rao ta ke matsayin mataimakiyar mai bayar da umurni.
Sun yi aure ne kuma a watan Disamban 2005.