Wanda Zai Gaje Ni Sai Ya Fini Rushe Gidaje – Inji Nasiru Elrufai


Yace wasu mutanen sun tsane shi saboda rushe-rushen da yake yi, har suke fatan kifewar gwamnatinsa.
Gwamna Elrufai wanda yayi wannan bayani ranar Alhamis a yayin wata hirar shi da aka sanya a gidan rediyo, ya ce yanzu mutane da dama suna jin daɗin irin ayyukan raya birane da gwamnatin shi ke yi a yankuna da dama na faɗin jihar.
Elrufai ya ƙara da cewa gwamnatinsa tafi sha’awar yin ayyukan raya ƙasa a maimakon a riƙa tara mutane ana raba musu kuɗaɗe da sunan bada tallafi ko gina mutane, kamar dai yadda muka samu daga jaridar Dailytrust,yayinda mu kuma mun dauko wannan labari daga Jaridar arewamobile
“A lokacin da muka fara aiki akan gyaran makarantu sai suka ce munƙi gyara hanyoyi. Yanzu kuma da muka zo muna gyaran hanyoyin sai suke cewa wai bama bawa mutane tallafin sana’o’i.
“Indai wai har sai mun riƙa bi muna raba ma mutane kuɗaɗe da dare da sunan tallafi, to lallai sai dai su cigaba da zaginmu.
“Al’ummar da muke yin aikin dominta ta gamsu da abubuwan da muke yi.
Gwamnan yace mutane suna ganin kamar cewa idan akayi zaɓe wani gwamnan ya hau za’a daina rushe-rushen, “ina fatan wanda zai zo bayana yayi rusau fiye da yadda nayi.”
Ya roƙi magoya bayanshi su cigaba da yi mishi addu’a don fatan samun nasara a harkokin mulkin shi.
Mutane da dama sun koka kan yadda suke ganin cewa gwamnan ya jefa mutane da dama cikin mawuyacin hali sakamakon rushe musu gidaje. Sai dai gwamnan ya ce yana yin duk abinda yake yi ne don cigaban mutane.