Labarai

Tsadar Rayuwa Da Yunwa Da Rashin Kudi Yana Karuwa

Hoto Daga facebook : President Muhammad Buhari

A gaskiya talakawan Nigeria na fuskantar barazanar rayuwa wanda ya fi na garkuwa da mutane da ta’addanci muni, barazanan kuwa shine yunwa, tsadar kayan abinci da na masarufi da kuma karyewan darajar naira
Hakika yunwa wani abune da ‘dan adam ba zai taba iya jurewa ba, sai da abinci ake rayuwa, na fahimci cewa a cikin wannan watan talakawan Arewacin Nigeria na fuskantar barazana na yunwa da rashin abinci da kuma rashin kudi da tsadar rayuwa
Idan kudin ya samu ana sayen abinci da tsananin tsada, sannan gashi ruwan sama yaki samuwa da wuri balle ayi noma, wanda hakan na nufin wahalar abinci da tsadar rayuwa da za’a fuskanta nan gaba sai yafi muni
Ya kamata Gwamnatin Maigirma shugaban kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya tayi gaggawan daukar mataki akan wannan matsala
Wannan halin da ake ciki zai iya jefa talakawa zuwa ga aikata munanan laifuka, sannan makiya zaman lafiyar Nigeria zasu iya amfani da halin kunci da ake ciki su bijiro da kudurinsu na wargaza Nigeria talakawan da suke shan azaba su goyi bayansu
Ya kamata Gwamnatin shugaba Buhari ta fitar da kudi, sannan a samar da tsarin da za’a samu control na hauhawar farashin kayan abinci a kasuwa, sannan idan akwai manyan ayyukan da ya kamata Gwamnatin tarayya ta dakatar da aikin a fitar da kudin a samawa talakawa sauki su sami abinci, to ya dace ayi hakan ba tare da bata lokaci ba.datti Assalafy babban shahararen marubucin nan ya wallafa a shafinsa na facebook
Muna rokon Allah Ya tausaya mana, Ya kawo mana sauki da mafita na alheri Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button