Labarai

Muna da damar ƙera wayoyi na zamani da layuka a Najeriya – Pantami

Ministan Sadarwa na Najeriya Isa Ali Pantami ya ce ƙasar na da damar da za ta samar da layukan wayar salula wato SIM card da kuma wayoyin hannu na zamani (Smart Phones) don kasuwancinsu a nahiyar Afirka.
Pantami ya bayyana haka ne yayin wani taro da wata majalisar ‘yan jam’iyyar APC mai mulki ta shirya a Abuja ranar Alhamis, kamar yadda kamfanin labarai na Bbchausa ya ruwaito.
Majalisar ta shirya taron ne ga ministocin gwamnati domin bayyana ayyukan da suke gudanarwa a ofisoshinsu.
Da yake jawabi a wurin taron, Pantami ya ce nan gaba kaɗan za a daina shigar da kashi 60 zuwa 70 na kayayyakin da ake amfani da su a ɓangaren sadarwa zuwa Najeriya daga ƙasashen waje.
Ya ce ƙasar na da ƙarfin da za ta iya samar da layin waya miliyan 200 a duk shekara.
“Mun samar da wani tsari na ƙera aƙalla kashi 60 zuwa 70 na abubuwan da muke buƙata a ɓangaren sadarwa nan da shekara biyu ko uku saboda za mu fara ƙera su a cikin gida, kuma har mun fara,” in ji shi.
“Lokacin da gwamnatin nan ta hau mulki, hatta layukan salula sai an shigo da su daga ƙasar waje. Yanzu gwamnati ta samar da yanayin da ake iya samar da su da kuma ƙera wayar salula ta zamani ba wai kawai don amfanin cikin gida ba, har da nahiyar Afika.
“Yanzu haka a Najeriya, muna ƙera wayoyin salula na zamani.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA