LabaraiSports

Menene Yasa ‘Cristiano Ronaldo’ Ya Kautar Da Lemon Coca-cola Daga Gabansa? ~ Awaisu Al’arabee fagge

Advertisment

Daga cikin ƴan uwanmu musulmi masu daukin ganin musulunci ya samu cigaba, suna ta yada wani bidiyo na shahararren dan kwallon kafa, Cristiano Ronaldo, yayin da ya kautar da kwalaben lemon COCA-COLA guda biyu da aka ajiye masa, kuma ya bar Ruwa a gabansa.
Da yawa daga cikin yan uwanmu masu kishin addini, suna farin ciki da hakan, domin suna ganin RONALDO yayi hakan ne domin nuna ƙyamar sa ga ƙasar Isra’ila, wadda itace ke da mallakin Kamfanin na COCA-COLA.
Amma a bisa bincike na hakika, shi Ronaldo bai dauke wancan lemo daga gabansa domin nuna kyama ga Isra’ila ba. Yayi hakan ne domin nuna ƙyamar sa ga ire-iren abubuwan da suke iya zama barazana ga lafiyar jikinsa.
Ko mu anan, ana jan hankalin mu akan rage shan lemuka musamman masu GAS, ballantana mutum irin Cristiano Ronaldo Wanda lafiyar jikinsa itace jarinsa.
Dukkan jaridun da suka rawaito labarin, sun bayyana cewa Ronaldo ya kyamaci Coca-Cola ne saboda lafiyar sa, domin ya nunawa al’umma yadda yake taka tsantsan da jikinsa. Idan ban manta ba, a kwanakin baya, anyi hira da Ronaldo da kuma ƴaƴan sa, a cikin abinda ɗansa ya fada, yace babansa ya hana shi shan lemuka da Chocolate….. Kenan kula da lafiya ne ya haifar da kin Coca-Cola.
A wata majiyar kuma, ance Shi Ronaldo ya saka hannu akan yarjejeniyar Talla da Kamfanin PEPSI, wanda shi Pepsi Kuma shine babban kishiya a wajen Coca-Cola. Kenan ya dauke lemon domin kada ya yiwa kishiyar Pepsi Talla.
Koma dai yaya ne, bincike ya tabbatar da cewa ba domin Kasar Isra’ila yayi abinda yayi ba. Wani abu ne daban.
A nan nake cewa, ya kamata mu musulmi mu zama wayayyu, mu taimaki addinin mu, mu yada shi da abinda yake na gaskiya, ba na jita-jita ba.
Yin amfani da jita-jita wajen bayyana nasarorin mu, abu ne da zai jawowa addinin mu jin kunya a idon duniya.
Allah ya taimaki musulunci da musulmi, ya kaskanta kafirci da kafirai.
Awaisu Al’arabee Fagge
17-06-2021

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button