Dan kwallo A Shehu Ya Auri Yar Fim Naja’atu wanda Tayi Fim Din Murjanatu Yar Baba
Majiyarmu ta samu wannan labarin na tabbatar da cewa wannan yarinyar Naja’atu Muhammad Najlat wanda akafi sani da Murjanatu Yar Baba yar wasan kwaikwayo ce ga bayyanin da shafin Kannywood exclusive sunka wallafa a shafinsu na sada zumunta.
“A yau ne aka daura auren Fitaccen Dan wasan kwallon kafa a arewacin Nijeriya, wato Abdullahi Shehu, da Amaryar sa wadda jarumar Finafinan Hausa ce mai suna Naja’atu Muhammad Suleman, wadda aka fi sani da “Murjanatu ‘yar Baba”
An daura auren bayan an gama sallar Juma’a a garin Kano.
Naja’atu, ta fara fitowa a Finafinan Hausa, tun tana ‘yar shekara 10.
Kadan daga cikin Finafinan da fito sun hada da ” Murjanatu ‘Yar Baba, “Auren Gaja”, “Hakkin Rai”, “Harira” da sauran su”
Muna yiwa wannan ango da amarya fatan Alkhairi Allah ya bada zama lafiya amen.