Da ƊUMI ƊUMINSU: Wata Kotu a ƙasar Faransa ta Yanke wa Mutumin da ya Shararawa Shugaban ƙasa Makaron Mari
An gurfanar da Mutumin da ya gaurawa Shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Makaron Mari yayinda yazo gaisawa dashi.
Bayan Alƙali ya saurari Lauyan wanda ake ƙara da shi wanda ake ƙarar Alƙali ya yanke hukunci, Lauyan yace wanda yake karewa ya Mari Makaron ne bisa dalilai guda biyu.
Kamar yadda zuma times hausa na wallafa a shafinsu na facebook na cewa,na farko Doka ta hana gaisawa hannu da hannu a ƙasar ta Faransa saboda cutar Korona, na biyu kuma dokar tace ana bada tazara ta aƙalla tsawon mita Ɗaya tsakanin Mutum da Mutum domin kariya wanda ba’a girmama ba.
Da haka wanda ake ƙarar ya Sha Inda Alƙali ya yanke hukuncin Tarar kudi Euro Dubu Ɗaya da Ɗari Biyar, a maimakon zaman gidan waƙafi na Watanni Ukku akan hukunci cin Mutunchi a bainar Jama’a.