Bani da sha’awar yin Takara amma zamu faɗa wa Al’umma wanda ya dace su Zaɓa- Sarki Sunusi
Babban Khalifan ɗarikar Tijjaniyya a Najeriya Muhammadu Sanusi ll ya ce ba shi da ra’ayin neman wani muƙami a Najeriya amma zai ci gaba da faɗakar da al’umma a kan irin shugabannin da suka cancanta a zaɓa.
Sarki Sunusi ya bayyana haka ne, a hirar sa da BBC Hausa, ya bayyana hakane a wani taron Muƙaddimai da kuma Shaihunnan Ɗarikar a karon farko tun bayan naɗa shi mukamin Khalifan.
Sunusi ya ce wannan ra’ayin nasa ba yana nufin ya shiga siyasa ba ne.
Yace Idan muna da waɗanda muka amince muka ce za su yi wa al’umma aiki za su gyara ƙasa, sai a hadu wuri ɗaya a taimaka musu – wannan ba shiga siyasa ba ne aiki ne na gyaran ƙasa da gyaran al’umma” inji shi
Ya cigaba da cewa rashin yin hakan na iya jefa mutanen Najeriya cikin babban haɗari da ƙalubalen rayuwa.
Ya ce ya zama wajibi a bayar da fifiko wajen samar da ilimi musamman ga ƙananan yara kafin a iya magance matsalolin da ƙasar ke ciki.
A cewar sa idan babu ilimin nan, yaran nan da muke ganinsu ba mu sa su a makaranta ba, yayan wadansu ƙabilu suna can suna makaranta, nan gaba waɗan nan yaran sune za su kafa kamfanoni, yaranmu su zama leburorinsu,” in ji Muhammadu Sanusi ll