Kannywood

Ba don Afakallahu ba, da yanzu Kannywood ta zama tarihi

A MATSAYI na na ɗan jaridar da ya daɗe ana fafatawa da shi a masana’antar finafinan Hausa, na sha yin rubuce-rubuce, musamman dangane da makomar Kannywood a mahangar kimiyyar zamani, duk da yake a baya ‘yan fim sun sha fama da ƙalubale kala-kala, har ta kai ga wasu sana’ar ma ta gagare su kwata-kwata.Ban mantawa a wancan lokacin, Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da su ka janyo wa masana’antar fim tarnaƙi.
Har na tuna da Malam Rabo, tsohon shugaban Hukumar Tace Finafinan, da ya lashi takobin ganin bayan harkar fim gaba ɗaya a yankin arewacin Nijeriya ba ma Jihar Kano kawai ba. Ya yi amfani da kujerar sa wajen fatattakar ‘yan fim daga Kano, inda su ka yi ta hijira zuwa wasu garuruwa domin tsira da mutuncin su. Ya karya ‘yan kasuwar finafinai, ya tura ‘yan fim da mawaƙa da marubuta da dama zuwa gidan yari, ciki kuwar da ni kai na.
‘Yan fim sun sha shirya tarurrukan yin addu’o’in neman mafita daga uƙubar da hukumar ta sanya su a wancan lokacin.
Ba zato ba tsammani, Allah ya yi masu gyaɗar Dogo, inda Gwamna Ganduje ya zaɓi ɗaya daga cikin masu ruwa da tsaki a harkar finafinan Hausa, Isma’il Na’abba (Afakallahu), a matsayin shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano mai ci yanzu.Da yawa sun zuba ruwa a ƙasa sun sha, wasu sun yi yanka saboda murna, wasu sun shirya walima, kasancewar wanda ya san mutuncin su da na sana’ar su ke kan mulki.
Ko tantama babu, Afakallahu ya taka rawar gani fiye da da yadda ake tsammani ta fuskar inganta harkar fim, da kuma ƙoƙarin goge baƙin fentin da a baya aka goga wa ‘yan fim, da ƙarfi da yaji aka haddasa ƙiyayya tsakanin su da mutanen gari.
A ƙarƙashin jagorancin Afakallahu a hukumar ne ‘yan fim su ka fara samun shiga a harkokin gwamnati, har ta kai ga ana ba wasun su muƙamai, ana kuma sauraren shawarwarin su a gwamnatance.
Sai dai kash! daga cikin mutanen da su ka shugabanci Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, babu wanda ya kai Afakallahu fuskantar ƙalubale daga abokan sana’ar sa ‘yan fim. Wannan kuwa ba ya rasa nasaba da abin da masu iya magana ke cewa, ‘Ido wa ka raina? Ya ce wanda na fi gani kullum.’
Ni dai na san a tarihin Kannywood, ba a taɓa samun lokacin da ‘yan fim su ka samu mahaukatan kuɗi kamar zamanin Afakallahu a Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ba. An ce idan ba ka san gari ba saurari daka. Zan kawo hujjojin da na dogara da su na cewa ba don Afakallahu ba, da yanzu Kannywood ta zama tarihi.
Ina buƙatar mai karatu da duk wani ɗan fim ya karanta ra’ayi na cikin adalci babu son zuciya.
Bayan Afakallahu ya zama shugaban Hukumar Tace Finafinai, a baya na gaya maku yadda ɗaukacin ‘yan fim su ka yi ta murnar nasu ya samu. Sai dai kash! wani abu da mafi yawa ba a sani ba shi ne Kannywood ta na da wata ɗabi’ar da duk wani ɗan fim ya san da ita, amma mafi yawa a kan kauda kai saboda tsananin son zuciya.Ni a fahimta ta, da yawa ‘yan fim sun zaci zuwan Afakallahu a hukumar zai ba su damar baje kolin su yadda su ke so, ba tare da doka ta hau kan su ba saboda a yau ɗan fim ne ke shugabancin hukumar.
Ina ɗaya daga cikin masu kiran Afakallahu su yi mashi nasiha game da duk wata matsala da ta auku tsakanin shi da abokan hulɗar sa, amma a matsayi na na ɗan jarida dole ta sa na dawo na yi karatun ta-natsu, to a nan ne na yi wa Afakallahu uzuri.
Na farko dai, Afakallahu Allah ya jarabce shi da shugabancin da ya zame mashi tamkar murhu.A wannan muƙami da ya ke riƙe da shi akwai haƙƙoƙin mutane uku da su ka rataya a wuyan shi. Na farko dai akwai haƙƙin gwamnati, wadda ta zura ido ta ga shin zai iya gudanar da ayyukan da ta ɗora masa ko a’a?Na biyu, akwai mutanen gari, waɗanda ake yin finafinai da waƙoƙi ko rubuce-rubuce domin su, kuma dole ya sauke nauyin sa-ido a kan irin abubuwan da za su kalla ko su saurara ko kuma su karanta. Rukuni na uku shi ne ‘yan fim, waɗanda ya zama wajibi Afakallahu ya kare muradin su, domin su ne musabbabin kafa ita kan ta hukumar.To inda matsalar ta ke shi ne duk duniya babu wanda bai san Afakallahu a matsayin ɗan fim ba, don haka sai wasu ke ganin ko ma me ya faru, bai kamata a ce dokar shi ta na shafar ‘yan fim ba.
Na taɓa kiran shi na yi masa nasiha dangane da wata rigima da ta faru tsakanin sa da wani babban mawaƙi, amma tambayar da ya yi min sai ta kashe min jiki. Tambayar da ya yi mani kuwa ita ce: “Aliyu Gora II idan ban yi wa gwamnati da jama’ar gari da sauran ‘yan fim adalci ba, za ka iya beli na a gaban Allah ranar tashin kiyama?” To daga nan jiki na ya yi laƙwas, don na san an zo ƙarshen iyawa ta.
A matsayi na na ɗaya daga cikin ‘yan jaridar da su ka taka rawa ta fuskar ci-gaban Kannywood, ban yi mamakin abin da ke faruwa da Afakallahu ba a yau, domin mu ma ‘yan jarida hakan ta faru da mu a baya, inda aka yi ta kyarar mu, ana yi mana kallon mu maƙiyan industiri ne ma.
Ban mantawa da lokacin da ‘yan fim su ka taru a Zoo Road, su ka yi wa mujallar Fim Al-Ƙunut. Ban mantawa da lokacin da aka haramta wa kowane ɗan fim yin hira ko wata mu’amala da mujallar Gidauniya. Ban mantawa da lokacin da duk industiri aka haɗe wa Ali Nuhu kai a kan harkar fim.Ni kuma na yi imani har ga Allah, waɗannan mujallun sun taka gagarumar rawar da tarihin Kannywood ba zai taɓa cika ba tare da su ba.
Wato wani babban abin da ya janyo rashin haɗin kai a Kannywood shi ne duk wanda ya samu ɗaukaka, to shi fa daga nan ya fi ƙarfin wani ya kafa doka ya bi a industiri. Na san irin wahalar da shugabannin MOPPAN su ka sha a baya, musamman wajen tabbatar da haɗin kan ‘yan fim, amma da yawa komai girman muƙamin ka, idan jarumi ya fi ka samun kuɗi, to ya fi ƙarfin ƙungiya ta kafa doka ya bi, tunda shi ake yayi.Ina so a sani cewa muƙamin da Afakallahu ke kai a yau ba na ƙungiya ba ne, na gwamnati ne, kuma da zarar ya saɓa dokar gwamnati, babu abin da ya rage illa ta kore shi, ƙarshe ma a sake ƙaƙaba wa ‘yan fim wani ƙasurgumin maƙiyin sana’ar kamar yadda ta taɓa faruwa a baya. Don haka, ni a gani na, ta kowace fuska ka kalli Afakallahu, kasancewar shi shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano alheri ne ga ɗaukacin ‘yan fim na arewacin Nijeriya, ba ma Jihar Kano kawai ba.
Bahaushe dai na cewa naka sai naka, kuma mutum ba ya sanin muhimmancin abin da ke hannun shi sai ya rabu da shi.Duk wata tsangwama da Afakallahu ke fuskanta a industiri, babu wani shugaban MOPPAN da bai fuskanci irin ta ba a baya.
Ya kamata mu yi wa kan mu ƙiyamullaili, mu fahimci juna, domin wata rana ba Afakallahu ba ne a wajen, kuma babu wanda ke da tabbacin irin wanda zai maye gurbin shi.
Na tabbata babu wani ɗan fim da zai iya kallon ƙwayar ido na ya gaya min cewa wai Afakallahu bai taka rawa ta fuskar cigaban Kannywood ba. Wani lokaci dole ta ke sa Afakallahu ya shiga hurumin ‘yan fim wajen daidaita al’amurra, domin shugabanni sun zura ido abubuwa na taɓarɓarewa, sannu a hankali har yaran sun fara jin ƙarfin su ya kawo, don haka, babu wanda ya isa ya hana su yin abin da su ke so, domin da jarin su su ka shigo harkar.
Mafi yawa ba mu cika son doka ta hau kan mu ba, kawai saboda rashin sanin muhimmancin shugabanni.
A rubutu na na gaba, zan yi ƙoƙarin kawo maku jerin ayyukan ci-gaban Kannywood da Afakallahu ya assasa. Kada kuma a manta, har gobe duk wani ɗan fim gaban shi ya na faɗuwa da zarar ya ji an ambaci sunan ‘Rabo’. Na tabbata babu mai jin haka a kan Afakallahu. Me ya sa?
* Aliyu A. Gora ne tsohon Editan mujallar Fim.inda munka dauko wannan rubutu daga mujallar fim.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button