An Kama Masu Taimakon Barayin Daji Da Abinci
Sarkin Yakin Nigeria DCP Abba Kyari ya samu nasaran gano wata masana’antar biredi a garin Galadimawa dake karamar hukumar Birnin Gwari jihar Kaduna wanda ake kaiwa barayin daji masu garkuwa da mutane
Ana buga dubbanin biredi a wannan gidan biredi dake Galadimawa, wanda ake dauka a mota a shiga jeji a rabawa manyan sansanin barayin daji masu garkuwa da mutane a Kaduna
Sarkin Yaki DCP Abba Kyari ya cafke matasa hudu da suke wannan bakar sana’a na sayarwa barayin daji biredi, ga sunayensu kamar haka:
1- Hassan Magaji
2- Abubakar Ibrahim
3- Auwal Abubakar
4- Ibrahim Kabiru
Idan an buga biredi da yawa, sai su dauka su nufi jejin Damari, anan ne zasu karkasa zuwa ga sauran manyan sansanin masu garkuwa da mutane dake Kaduna
Mai gidan biredin Hassan Magaji ‘dan shekara 29, yana da mata biyu, yace ya zabi ya dinga sayar da biredinsa wa barayin daji ne saboda yafi kawo kudi, suna sayen biredin da tsada
Bayan an kama Hassan Magaji ya bayyana nadamarsa, yace soyayyar sabuwar amaryarsa da ya aura ne ya kaishi ga hada kai da barayin daji don ya samu kudi mai yawa da zai faranta ran amaryansa, saboda yana matukar kaunarta, amma wai yanzu yayi nadama
Jama’a wannan shine nadama marar amfani, al’amarin Hassan Magaji yazo karshe, amaryansa da yace yana matukar kauna dole su rabu ta auri wani, zai karasa rayuwarsa a gidan yari, ita kuma amaryan zata auri wani, yana kwance a dakin kurku wani kuma yana kwance da amaryansa a dakinta
Ko ba komai akwai darasi cikin wannan abu da ya faru, ya kamata matasa ayi kokari wajen yaki da zuciya, kowa ya tsaya iya matsayin da Allah Ya ajiyeshi, a nemi halal a guji neman kudi ta mummunan hanya saboda gujewa samuwar ranar da za’ayi nadama marar amfani kamar yadda Hassan Magaji mai gidan biredi yayi a yanzu majiyarmu ta samu daga shafin shahararen marubuci datti assalafy
Muna rokon Allah Ya tsare mana imanin mu, Ya bamu halal, Ya nesanta haram daga garemu Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum