Tirƙashi: Dubai ta bayyana abaya mafi tsada a duniya kan Naira biliyan sittin da miliyan tamanin (60,880,000,000)
Rigas wadda adon jan lu’u-lu’u mai tsananin sheƙi kuma maras abin kushewa, anyi mata adone da lu’ulu’u, wanda ya ƙawata ta, mai tsara sutturar Burtaniya Debbie Wingham ce ta tsara shi.
Rigar tana ɗauke da zoben dinki sama da 200,000, dukkansu an dinke su da hannu da zaren farin karat 14-karat na lu’ulu’u
Kamar yadda shafin yanar gizon Wingham ya tabbatar, abayar ta ƙunshi jimillar duwatsu masu daraja 2000, waɗanda suka haɗa da lu’u lu’u fari karat 2.
Sai kuma baƙin lu’ulu’u karat 50, haɗe da fararen lu’ulu’u marasa sirki biyu, sai ƙarafa masu matuƙar daraja da kyau, da kyakkyawan jajayen lu’u lu’u da kuma na lu’u lu’u na musamman guda1899.
Tare da babban jan lu’u-lu’u, rigar anyi ittifaƙin cewa darajar ta, takai kimanin dala miliyan 16 kwatankwacin Naira biliyan sittin, da miliyan ɗari takwas da tamanin (N60,880,000,000), sannan tana da siffofin fararen lu’u-lu’u masu launin ɗirson jajayen karafunan alfarma carat biyu.
Masarautar Dubai ce dai da ke da arzikin mai a ranar Laraba ta gabatar da abaya mafi tsada a duniya (riga), wacce darajarta ta kai dala miliyan 16.
Yanzu idan aka ware kuɗin wannan riga, ita kaɗai kawai zata iya yin fiye da rabin kasafin ƙudi na jihohin kasar nan da yawa.
Wannan shine yake nuna asalin yadda darajar wannan abayar take.
Haƙika wannan riga, wani kaya sai amale, jaridar mikiya na kawo wannan rahoto.