Rai Ɓace! Mansurah Isah Tayiwa Allah Isa Gasu …….
Tsohuwar Jarumar masana’antar Kannywood Mansurah isah uwar gidan jarumi sani musa danja ranta yayi matukar baci wanda har kai ga Allah ya isa ga wadanda sunka ci amanarta,ga abinda ta wallafa a shafinta na sada zumunta Instagram.
“Ya Allah kana kallon komai, ba abinda yake wuce ka. Dan wannan kudin da akace a bamu, da bai fi karfin suba. Shi dinma hana mu sukeyi.
Haka aka bada abinci a bamu amma suka ajiye har sai da ya lallace dan bakin ciki da rashin imani da sanin darajan dan adam da irin yunwan da ake fama dashi.
Gashi nan kullum sai labari mukeji an raba dubu 20, dubu 500, miliyan daya amma ba Wanda zai gaya maka ya samu. Haka lokacin lockdown akace an bawa mutane dubu 25, each amma wallah banda labari ba abinda mukaji, da mukaje kauye muka tambaya akace ai mutum 20 kawai aka bawa, sukace zasu dawo shikenan,
Sun dauki hoton mutum ashirin kawai sunce sun bawa mutum miliyan.
Allah ya isa
Alah ka saka mana
Allah ka zama gatan mu
Allah ka jikan mu
Allah ka gyara mana kasar mu.”