Najeriya ta sake karya darajar naira a hukumance
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya karya darajar naira a hukumance sakamakon fara aiki da ya yi da sabon tsarin canji na Nigerian Autonomous Foreign Exchange (NAFEX).
Kamar yadda bbchausa na ruwaito.CBN ya rage darajar kuɗin da kashi 8 cikin 100, inda yanzu take N410.25 kan kowace dala ɗaya.
Kazalika bankin ya bayyana sauyin ƙarara a shafinsa.
Mako biyu da suka wuce kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito cewa bankin zai karya darajar naira ta hanyar sauka daga kan N379 kan kowace dala ɗaya domin tsayar da farashin nairar guda ɗaya a kasuwa.
Wannan sauyin na nufin daga yanzu kasuwa ce za ta dinga fayyace darajar naira ko kuma farashinta yayin canji.
Najeriya ta daɗe tana amfani da tsaruka mabambanta wajen canjin kuɗaɗen ƙasar waje, abin da ya sa CBN ya mayar da hankali kan tsari guda ɗaya kenan a yanzu.
Babu tabbas game da yadda darajarta za ta kasance a kasuwar bayan fage, yayin da a ‘yan kwanakin nan nairar ke kaiwa har kusan N490 kan dala ɗaya.