Kannywood

Martanin Aminu Alan Akan Rarara ! Fadi Alheri Ko kayi Shiru,ko kachi Ubanka

A yau ne Majiyarmu ta samu labarin akan irin jawabin da jarumin yayi akan dauda kahuta rarara a shafinsa na Instagram ga abinda nake cewa.
“RARARA…..FADI ALHERI, KO KAYI SHIRU, KO KACHI UBANKA…Bari inyi da hausa saboda kowa ya samu. A gaskiya wannan industry tamu ta Kannywood sai a hankali. Duk abinda muttum zai aikata komai kyawunsa da alherin abun sai dole an samu masu gutsuru tsoma. A tarihin Kannywood tun daga lokacin pioneers irinsu Iyantama, Auwal Sarauniya, Danazimi Baba da sauran su, kawo izuwa yau, ba’a taba samun muttum wanda yake dibar tsabar dukiyarsa, guminsa daya nemawa kansa yake rarrabawa jama’ar masana’antar kamar Dauda Kahutu Rarara ba.
A irin wannan lokaci da ake cikin matsalar kunchin rayuwa da tsabar talauchu, Ya baiwa mutane da dama kyautar motoci kala kala. Banda sunayan jama’a yan film na da dana yanzu da ake jerowa ake raba musu kudade daga dubu dari dari, hamsin ko talatun wanda ta hakan yake kashe miliyoyin kudade. Yana yine fissabilillah. A dukiyarsa, a aljihunsa, ba tare da neman komai a wajan wadanda ya baiwa ba. Yi kawai yake dan Allah. Ba siyasa yake ba bare kace yana neman kuri’ar ka.
Irin wannan halaye nasa nai magana a rubutun da nai masa a jaridar turanchi yau fiye da wata shida baya.
Amma maimakon muyaba masa, wasu na fadar ai Riyya ne abinda yake. Indai haka riyya take to dan Allah suma sauran masu hali irinsa su dunga irin wannan riyya indai al’umma zasu amfana. Ba maganar riyya, hakan da yake zai bawa wasu kwarin gwiwwa suma su fito su taimaka, kuma ana nunawa duniya cewa muna kishin junanmu.
Ayanzu a industry, ko dai ka yabi alherin irinsu Rarara da Abdulamart acikin jama’a ko kayi shiru. Idan zagi ko baka zaka fada akansu to ka buya kai da abokin yinka kuyi tare ku tashi kubar azumin ku awajan, amma idan kayi cikin mutum uku ko hudu, wallahi sai wani yaci UBANKA..
Wasu sunche ai kudin waka ne, kudin banza. Tirrr. Ai wani ko tsinko kudin yake bazai iya abinda Rarara yakeyi ba, bare waka. To waka ai ba karamin aiki bane. Abune ne na Creativity and Talent. Waka abace da sai anji jiki, an bawa kai wahala wajan tunani da kirkira. To a harkar showbiz bawani abu na sauki.
Koma maye, halak dinsa ne, dukiyarsa ce, gumin sa ne yake nemowa yake yiwa al”umma. Banda wanda yake aboye, wadanda Allah kadai yasan yawansu. Fatan mu sauran masu motsi, suyi koyi dashi…”

 

View this post on Instagram

 

A post shared by Realahlan jinsee (@realahlan)

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button