Jamia’ar Wudil za ta hukunta mazan da suka yi wa ɗaliba ihun saka abaya
Mahukuntan jami’ar kimiyya da fasaha ta Wudil a Jihar Kano ta ce za ta ɗauki “mummunan mataki” kan ɗaliban da suka ci zarafin wata ɗaliba saboda ta saka rigar abaya.
Kamar yadda Bbchausa na ruwaito Cikin wata sanarwa da makarantar ta fitar a jiya Talata, shugaban sashen harkokin ɗalibai ya nemi afuwar ɗalibar sannan ya buƙaci ta shigar da ƙara a hukumance domin neman haƙƙinta.
A jiya Talata ne aka ga wasu matasa na jan abaya da wata ɗaliba ta saka tare da yi mata ihu cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan zumunta a wani wuri da aka ce cikin jami’ar ne ta Wudil.
“Hukumar Kano University of Science and Technology Wudil ta samu ƙorafe-ƙorafe daga shafukan zumunta game da wata ɗaliba da ɗalibai maza suka ci zarafinta saboda ta saka abaya,” a cewar sanarwar.
“Ni shugaban sashen harkokin ɗalibai zan ɗauki mummunan mataki a kan wannan lamari. Ɗalibai su sani cewa su ba hukuma ba ce da za su ci zarafi ko ɗaukar mataki kan wani, sai dai kawai su kai rahoto wurin jami’an tsaro.”
Sanarwar ta ce abaya ba ta saɓa wa dokar saka tufafi ta jami’ar ba, “saboda haka ɗalibar ba ta karya wata doka ba”.
Dear @ShehuProf the Humble Vice Chancellor of Kano University Of Science and Technology Wudil, this is a video of a female student being sexually harrased just because she was wearing an Abaya while passing through the male hostel around Area 1 axis, these pic.twitter.com/nAwvG6ypB6
— DR. SAMBO? (@Abdullahiabba_) May 25, 2021