Labarai

Hisbah ta kori babban jami’inta da aka samu da matar aure a Otal

Advertisment

Hisbah ta kori babban jami’inta da aka samu da matar aure a Otal
 
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kori babban jami’in ta Sani Nasidi Uba Rimo da aka samu da matar aure a ɗakin Otal.
 
Hakan na cikin wata takarda da hukumar Hisbar ta aike wa mai ɗauke da sa hannun babban jami’in mai lura da ma’aikatan hukumar Malam Sani Alasan.
 
Sanarwar ta ce, korar Rimo ta biyo bayan karɓar rahoton Kwamitin bincike kan zargin da aka yi masa da hukumar ta yi.
 
Sakamakon binciken kwamitin, la’akari da faruwar lamarin ya sanya tilas Hisbah ta ɗauki wannan mataki na korar sa daga aiki.
 
A watannin baya ne dai aka zargi Sani Nasidi Rimi da ɗaukar wata matar aure tare da kai ta wani ɗakin Otal a unguwar Sabon Gari.
 
Zargin da Rimon ya tabbatar da aikatawa yana mai cewa ya yi hakan ne domin ya gargaɗi mijinta.
 
Daga nan ne kuma rundunar ƴan sandan jihar Kano ta bakin mai magana da yawunta DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ta fito ta wanke Rimon, inda ta ce, eh haka ne ya kai ta Otal amma don ya tseratar da ita.
 
Sai dai kuma wannan bayani na ƴan sanda ya ci karo da sakamakon rahoton da kwamitin hukumar Hisbah ya fitar, bayan shafe tsawon lokaci yana ƙwaƙƙwaran bincike a kan lamarin.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button