HARKAR fim wata halastacciyar sana’a ce a cikin addinin Musulunci matuƙar za a kiyaye ƙa’idojin da ya kamata a bi, inji shugaban Zauren Malamai na Jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil.
Malamin ya bayyana haka ne a wajen taron buɗa baki da haɗaɗɗiyar ƙungiyar masu shirya finafinan Hausa ta Nijeriya (Motion Picture Practitioners Association of Nigeria, MOPPAN), reshen Jihar Kano, ta shirya a yau Lahadi, 2 ga Maris, 2021 a Kano.
A taron mai taken “Fim a Musulunci, Tasirin Sa Da Kuma Ƙalubale”, an kira malam mai faɗakarwa Ibrahim Khalil domin ya yi tambihi kan tasirin fim ga al’umma tare da bayyana wasu daga cikin ƙalubalen da ya kamata masana’antar ta tashi tsaye domin kawar da su.
Sheikh Ibrahim Khalil, a jawabin nasa, ya ce, “Sana’ar fim hanya ce mafi sauƙi wurin isar da saƙo tare kuma da yin tasiri ta cikin abin da mutane su ka kalla a cikin sa, duk da cewar wasu daga cikin malamai su kan soki fim wanda jama’a ba su gane ba cewar malamai ba sukar fim ɗin su ke yi ba illa su na sukar abin da aka nuna a cikin sa wanda bai dace ba.
“Amma shi fim karan kan sa ba shi da wani aibu, kuma hakan alhaki ne ga Hukumar Tace Finafinai da masu duba fim kafin ya fita ga jama’a, domin samar da abu nagartacce wanda ba za a soke shi ba ko bayyana wani aibun sa.”
Malamin ya ƙara da cewa, “A lokacin Daular Usmaniyya shekara kamar ɗari uku ko huɗu ko ma biyar da su ka shuɗe, an so a yi wani fim na Annabi Musa alaihisalam, wanda wasu Yahudawa su ka ce za su yi. Amma da aka tambayi Daular Usmaniyya sai su ka ce ba za a yi wannan fim ɗin ba, amma daga baya abin da malamai su ke kai a yanzu, hatta malaman Saudiyya, ta cikin littafin su ‘Allajinatudda’ima’, wato kwamitin fatawa na dindindin, sun yarda cewa za a iya yin fim, sai dai sun yi magana a kan abu guda biyu: idan Annabi sallallahu alaihi wa sallam ake so a yi fim a kan shi ko a kan wani Annabin da sauran sahabban sa, to wannan jarumin ba zai fito fili mutane su gan shi ba kuma ya yi aktin a matsayin su ba, sai dai ya zamana kamar yadda aka yi fim ɗin nan na Annabi Ibrahim wanda sai dai a ji maganar mutum amma suffar sa ba za ta bayyana ba. Amma duk wani wanda ba Annabi ba kuma ba sahabi ba to kowanne mutum zai iya fitowa ya yi aktin kamar su, wannan babu laifi.”
Da ya ke zayyano irin tasirin fim ga al’umma, Malam ya ce, “Fim ko sinima ba laifi ba ne a cikin Musulunci, sai dai idan abin da aka yi akwai laifi a ciki.
“Shi kuma fim wata hanya ce ta isar da saƙo domin akwai hanyoyin tura saƙo uku da mu ke da su, shi ne ko ka ji ko ka gani ko kuma ka karanta, shi kuwa fim ya haɗa waɗannan hanyoyi guda biyu tunda ta haɗa ji da kuma gani, kuma ita ce hanya mafi saurin isar da saƙo saboda mutum ya na ji kuma ya na gani.
“Bugu da ƙari, a kan samu wani ma mai ɗauke da rubutu, wato ‘subtitles’, kun ga kuwa an haɗa hanyar isar da saƙo guda uku kenan.
“Sannan ba za ka hana fim ba domin ba ka da wata hanyar isar da saƙo da sauri kamar fim. Shi ya sa malamai ba su taɓa haramta fim ba, sai dai su ce abu kaza a cikin fim bai dace ba kuma kai ba ka zauna ka ga fim ɗin har zuwa ƙarshe ba ballantana ka yi hukunci.
“Don haka fim ya na da tasiri matuƙar gaske ga al’umma wajen canza musu halayya ta hanyar kwaikwayo.”
Da ya ke zayyano irin ƙalubalen da ita kan ta masana’antar finafinan Hausa ta shiga, ya bayyana cewa, “Akwai rashin saka hannun gwamnati a cikin wannan masana’antar, kamar yadda wasu daga cikin gwamnatoci su ke yi na bada kuɗi domin a shirya fim kan doka da oda ko wani abu da ya sha wa mutane kai, musamman wasu daga cikin cututtukan da ya kamata mutane su sani da hanyar kariya ta hanyar shirya fim.
“Sannan akwai wani ƙalubale da mu kan mu malamai da mu ka tashi domin ganin an samar da wani ƙauyen shirya fim, wato ‘Film Village’ da gwamnati ta so ginawa amma da su kan su ‘yan fim ɗin aka yaƙe mu wanda kuma a da mun ɗauki alwashin tsayawa tsayin daka don ganin mun kare ta daga duk wani tunani da jama’a su ke a kai.
“Akwai ƙalubalen da har yanzu mawadata ba su gane cewar ana samun arziki a cikin masana’antar fim ba, ba su san kuma amfanin ta ba. Daga cikin ƙalubalen akwai yadda wasu daga cikin ‘yan Kannywood ke kambama magana ta hanyar rashin jituwa da wasu daga cikin jarumai wanda su ke yi da faɗa wanda kuma da zarar hakan ya faru za a fito ai ta yayatawa, wanda hakan bai kamata ba.
“Kana akwai ɗebo marasa hankali a cikin fim, ba wai masu hankali ba wanda kawai da zarar fim ya fito shi kenan, ba a zuwa a nemi wanda ya ke da cikakkiyar sana’a kan abin da fim ɗin ya ƙunsa kan a ce an fara fim ɗin domin samun ilimin yadda fim ɗin zai ja hankalin ‘yan kallo.”
Har wa yau Malam Ibrahim Khalil ya bayyana cewa akwai buƙatar samun ƙwarewa a cikin wannan masana’anta ta Kannywood wanda yanzu ake da ƙaranci.
Shi ma a nasa ɓangaren, mai riƙon muƙamin shugabancin ƙungiyar MOPPAN ta ƙasa reshen Jihar Kano, Malam Salisu Muhammad (Officer), a jawabin sa jim ƙaɗan bayan kammala taron ya bayyan farin cikin sa kan wannan gagarumin taron da ya jagoranta. Ya kuma shaida wa mujallar Fim maƙasudin shirya wannan taron faɗakarwar da kuma buɗe baki, ya ce, “Wannan taron mun shirya shi ne domin samar da haɗin kai a junan mu, sannan zai jaddada dangantakar mu, sannan kuma zai ba mu wata ƙima a waje wanda mutane su ke kallon kamar ba mu taɓa shirye-shirye irin wannan ba.
“Mu na so mu cimma abubuwa da dama kamar yadda mu ke so mu kalli ita kan ta harkar fim ɗin a Musulunce da kuma tasirin ta ga al’umma tare kuma da ɗaura ɗamara wajen ganin mun fuskanci ƙalubalen da ya ke damun Kannywood, sannan mu na so mu haska wa gwamnati cewar akwai abin da ya kamata ta taimaka, musamman yadda ake fama da rashin jari.”
Mujallar Fim ta ruwaito cewar jarumai da dama ne su ka halarci wannan taron wanda su ka haɗa da mata da maza irin su Ibrahim Mandawari, Auwalu Isma’il Marshal, Hassan Giggs, Kamal S. Alƙali, T.Y. Shaban, Sani Danja, Yakubu Muhammad, Bala Anas Babinlata, Ali Jita, Salisu Giɗaɗo, Umar Gombe, Shu’aibu Idris Lilisko, Isma’il Khalil Ja’en da sauran su.
A ɓangarena mata kuwa akwai Asma’u Sani, Hauwa A. Bello, Saratu Giɗaɗo, Teema Makamashi, Maryam CTV, Hadiza Kabara, Hadizan Saima, Maijidda Abbas, Ladidi Fagge, Aisha Abubakar da sauran su.
An ci an sha, an sada zumunci ta hanyar ɗaukar hotuna tare da zama teburi ɗaya wajen cin abinci wanda aka gudanar bayan an kammala sauraron jawabin Malam Ibrahim Khalil.
To sai dai mujallar Fim ta lura da cewa wasu daga cikin manyan jaruman da ke Kano ba su halarci wannan shan ruwa ba, inda aka danganta hakan da bambancin ra’ayin siyasa da ke tsakanin ‘yan fim ɗin.