Game Da Bidiyon Matasa Masu Dukan Ƴan Mata A Bauchi Ga Yadda Ainahin Lamarin Yake
Ga yadda ainahin lamarin ya ke don kaucewa gina hukunci a baibai.
Da farko ya kamata a fahimci cewar, da waɗanda aka daka ɗin da waɗanda su ka yi dukan dukan su akan layi ɗaya su ke. Ɓacin rana aka samu.
Su ƴan matan da aka gani ana jibga a bidiyon, ayari su ka yi daga unguwar su ta Dawaki, zuwa wata unguwar wato Ƙofar Dumi da zummar aikatawa wasu mata irin wannan abun da aka aikata musu.
Su ma da sun dama, fiye da wannan abun da aka musu ɗin za su yi wa waɗanda su ka hara. Su kuma waɗannan (mazan da ke dukan na su) ƴan matan su aka kaiwa harin.
Da aka ankarar da su akan an kawo musu hari har cikin unguwar su ta Kofar Dumi, kuma daga unguwar Dawaki (abokan gaban su) domin dama can akwai rashin jituwa a tsakanin su, sai wasu daga cikin su, su ka tari ƴan matan, su ka ja musu kunne da su fice musu daga unguwa, amma ganin mutum ɗaya biyu ne, su ka yi taurin kai. Su ka nuna sai sun je in da suka nufo don aikata abin da su ka yi niyya.
To, wannan ne ya tunzura matasan (Ƴan Sara Sukan) su ka ga an zo har unguwar su za a musu tsageranci, alhalin su tsagerancin ma su suka yanke mata cibiya kuma a ƙarƙashin ta su ke rayuwa. (Duk wanda ya san garin Bauchi, idan aka yi maganar harkar daba, kusan Kofar Dumi su na kan gaba wajen duk wata fitsara da fanɗara. Maza da mata, kuma duk hukumomi sun fi kowa sani. Saboda su na sa ɗaurin gindin wasu ƴan siyasa)
To, bayan nuna taurin kan ne, sai su (waɗannan matasa da su ka tare su, su ka yi wa ragowar ƴan uwan su kiran gaggawa, ba tare da sun ankara ba, suka dira a wajen ɗaya bayan ɗaya. Shugaban Ƴan Sara Sukar na Ƙofar Dumi, wato…. wanda dama cike yake da ƴan makwaftan unguwar ta su (Unguwar Dawaki) ya sa aka garzaya da su Majalisa/Jangul/Area/matattarar su) wannan Kangon da aka gan su, su ka yi musu wannan hukuncin mai kama da huce haushi.
Kuma saboda ka san lamarin babba ne, kuma isassu ne, ya sa aka kunna kyamara aka ɗauki bidiyon hukuncin da ya yi ɗin da nufin a turawa iyayen gidan ƴan matan su gani, a matsayin goron gayyatar ɗora ɗambar wata sabuwar rigimar idan sun shirya.
Wannan shine dalilin ɗaukar hoton bidiyon don bakanta ran abokan rigimar ta su na Unguwar Dawaki. Kuma ba iya duka ba ne kawai aka musu ba, har da aske mu su gashin kai da wasu abubuwan kuma. Hatta kuma… sai da aka ɗauki hoton bidiyon yadda aka yi, fitar da shi ne kawai ba su yi ba. Don COVER kamar yadda ɗaya daga cikin su ya shaida min.
MU FAHIMCI WANI ABU A NAN
Dama fa irin waɗannan su na faruwa a mafi akasarin yankunan Arewacin Najeriya in da ake fama da matsalolin kangararrun da su ka ƙunshi Ƴan Daba, Ƴan Kalare, Sara Suka, Ƴan Dinaya da Tsagerun Matasan Unguwa da dangogin su.
ABUN LURA
Waɗannan ƴan matan fa ba karuwai ba ne da suke sana’ar karuwanci kawai ba. Kamar yadda na ji wasu na maganar wai ƴan (Good Evening) ne.
Amma sai dai babu wacce ta ke gaban iyayen ta, kuma iyayen su ka isa da ita. Dukan su gagararru ne. Kuma har wata matattara ce fa da su, makamanciyar irin ta waɗanda su ka musu wannan dukan da ke ƙarƙashin tawagar iyayen gidan na su, Gayun unguwar Dawaki.
Kenan lamarin tamkar rigima da faɗa da yaƙi tsakanin abokan hamayya da juna ne, sai kuma aka samu wani yayi nasara akan ɗan uwan sa.
Yara ne da dukan su babu irin nau’in kayan mayen da ba sa sha irin ta mabugan na su. Kuma ga duk wanda ya ga bidiyon da ASIBITI ya naɗa, wace ce ko a fuska aka duba da ba a make take ba.
Waɗannan ƴan matan fa, babbar harka ko sana’ar su ita ce amfani da su da ake yi wajen safarar miyagun kayan maye, tun da su mata ne, su dinga sadar da su zuwa ga wasu sassa da wasu mutanen da ba za ka taɓa tsammani ba a ɓoye. Ciki har da matan auren da ke cikin gidajen mazan su.
To, sun je kai raraka ne wajen abokan adawa (ƙawayen su na can Kofar Dumi akan wata harkar su can ta banza) sai kuma rana ta ɓaci musu, reshe ya juye da mujiya. Abun da aka musun su ma shi su ka je yi. To, sai yaya kenan?
Akwai ɗaya daga cikin su wacce bazawara ce, har ƙaramin yaro ne fa da ita, amma ta jefa rayuwar ta cikin irin wannan ƙazantar.
Babu dama maganin biri sai karen maguzawa. Kuma muddin ka ƙi sharar masallaci, to, la shakka kuwa sai ka yi ta kasuwa.
Ko a iya alhakin bijirewa iyaye da watsar da tarbiyyar da aka ba su aka tsaya, shi kaɗai ya isa ya dinga bibiyar su har wannan sakamakon ya dinga biyo baya.
DAGA ƘARSHE
Babu wanda ba zai ji takaicin wannan abun da ya faru ba, saboda akwai nau’i na rashin jin daɗi yayin kallon faruwar abun. Amma idan aka yi la’akari da waɗanda su ka aikata hakan da kuma waɗanda aka aikatawan, to zai fahimci lallai ƙalubale ne babba ke gaban al’umma gaba ɗaya da musamman Hukumomi wajen yaki da ƴan Daba da masu shan miyagun ƙwayoyi da dillalai da masu safarar ta, mazan su da matan su irin waɗannan.
Don duk waɗannan abubuwan sakamako ne ya biyo bayan sakaci da aka yi har wasu su ka saki hanyar kirki su ka rungumi wannan baƙar rayuwa ta rashin ɗa’a a tsakanin su har su, kuma har su yi abu su ɗauka su na yaɗawa duniya ta na gani don nuna ƙarfin da su ka yi a babin aikata munanan laifuka.
Duk wanda ya ƙi jin bari, ai kuwa ba zai ƙi jin hoho ba.
– Ahmad Nagudu
#NaguduTv