Labarai

Cutar korona: An sake kafa dokar kullen korona a dukkan jihohin Najeriya daga yau Talata

Kwamitin shugaban Najeriya mai yaki da annobar korona ya sanar da sake kafa dokar korona da za ta shafi wasu bangarori na rayuwar jama’a, da zummar dakile cutar daga yaduwa.
Kamar yadda bbchausa na ruwaito. Daga ranar Talata, an rufe gidajen rawa da wuraren motsa jiki da sauransu a dukkanin faɗin jihohin kasar, saboda fargabar sake bazuwar cutar, a lokacin da ake ganin hakan na faruwa a wasu kasashen duniya.
Mahukunta a ƙasar sun jaddada matakan kariya ciki har da hana zirga-zirga daga ƙarfe 12 na dare zuwa huɗu na asuba.
Sun kuma nanata matakin hana tarukan mutane fiye da hamsin, sannan a wuraren ibada, dole ne rabin mutanen da wuri yake ci ne kawai aka yarda su yi shiga don yin ibadah.
Manajan gudanarwa na kwamitin kula da al’amuran cutar korona na shugaban ƙasa a Najeriyar Dr. Mukhtar Mohammed ta wayar tarho ya bayyana wa BBC cewa ba za su jira sai al’amura sun sake dagulewa ba kafin a fara tunanin me ya kamata a yi ba.
“Mun yi la’akari da irin abubuwan da ke faruwa a kasashen Brazil da Ajantina da Amurka, kai har ma da wasu kasashen Afrika inda ake samun karuwar masu kamuwa da wannan cuta, don haka muka ga dacewar dauakr wannan mataki tun yanzu don kare al’ummarmu,” a cewarsa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button