Bidiyo : ‘Yan Sanda Sun Kama Shahararren Mai Luwaɗi Da Kananan Yara Cikin Watan Azumi A Katsina
Rundunar’Yan Sanda ta jihar Katsina karkashin jagorancin kwamishinan yan Sanda Alhaji Sanusi Buba ta kama wani kasurgumin mai luwadi da kananan Yara, Muhammad Auwal Aliyu wanda aka fi sani da (Dan Mai Waina) dan shekara 41 da yake zaune a Unguwar Abbatuwa a cikin birnin Katsina.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isa ya yi baje kolinsa a helkwatar rundunar dake Katsina a yau Talata.
Gambo Isa ya kara da cewa aikinsa shi ne ya samu yara kanana, wadanda shekarunsa ba su wuce takwas zuwa goma ya dauke su ya dunga lalata da su, musamman cikin wannan wata na Ramadan da muke ciki ya ke aikata wannan barna. Mun kama shi kuma bai musanta ba, har ya koya ma wani yaro shima an Kama Shi yana lalata da yaro dan shekara ukku.
Da Muhammad Auwal Aliyu yake tattaunawa da manema labarai ya bayyana cewa wannan yaron na yi amfani da shi sau da dama, kuma ta bayan shi nake amfani da shi.
Auwal ya kara da cewa “Asiri ne wani boka ya taba bani, ina fasa kwabri daga Jamhuriyar NIjar zuwa Najeriya, idan na dauko kayan babu jami’in tsaron da zai tare ni, kuma kafin ya bani sai da ya yi amfani da ni, ya ce in cigaba da yi da kananan yara. Ban da abinda zan yi sai Allah ya fidda ni ya shirya mu baki daya. Tabbas cikin wannan azumin ne aka kama ni Ina luwadi. Ina da mata da yara” in ji Auwal Aliyu kamar yadda zaku saurara daga bakinsa ga bidiyo nan mun kawo muku
Daga Jamilu Dabawa, Katsina