Labarai

Bayan Shekaru Ashiri da Rasuwa Likafaninsa Baiyi Datti Ba Gawarsa ma Bata Lalace Ba

Alhaji Abubakar Suleiman ya rasu shekaru 20 da suka gabata a garin Jos bayan gajeruwar rashin lafiya.
An birne shi a wata maƙabartan da aka birne wadanda rikicin Jos ya rutsa da su a wannan lokaci.
Majiyar Zuma Times Hausa ta Daily Trust ta bayyana cewa, masu filin watau Kungiyar Jibwis ta bukaci filin don gida shagunan sayen kaya na zamani inda ta bukaci a fid da gawanwakin a canza masu makwanci.
Bayan cire gawanwakin 52 wadanda aka binne su a rami daya ne aka dawo kan gawar Alhaji Abubakar Suleiman wanda Sarkin Bukur ne a wannan lokacin sai mai jagorar cirewa, Alhassan Abdullahi ya ce sai ya fara jin wani abu a jikinsa wanda ya yi ta ba shi mamaki bai furta ba.
Ya ce yana budewa sai ya ga likafaninsa fari tas babu datti, sannan makwacinsa kamar an share.
Sannan ya ce, “da na dauki gawar ba kamar na sauran da suka Lalace, suka kararaye na saka kasusuwarsu a buhu ba, tasa kamar yanzun aka birne shi babu abinda ya same jikinsa, bai bushe ba, bai kararaye ba.’
Bincike daga iyalansa ta bakin dansa, Alhaji Suleiman Magajin Bukur ya ce, an san mahaifinsu da saukin kai, ba ruwan shi da fada da kuwa, ya ce mutum ne mai hakuri da ke fara gai da talakansa kafin a gaishe shi. Kuma yana raye bai taba daukan ya fi kowa ba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button