Labarai
An cire Bill Gates daga jerin masu kudin Duniya bayan da ya saki matarsa
Attajirin Duniya, Bill Gates ya fita daga jerin masu kudin Duniya na Jaridar Forbes bayan sakun matarsa, Melinda.
Jaridar ta dauki wannan matakin ne biyo bayan sanarwar Rabuwar Melinda da Gates bayan shekaru 27.
Ana tsammanin dai Melinda zata kwashi kusa Rabin dukiyar Bill Gates idan aka kammala maganar rabuwar auren nasu.