Labarai

Yawan Haihuwa ne yasa Nageriya ta Gaza Samun Cigaba ~Inji Sanusi Lamido

Tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana cewa da wuya Najeriya ta samu ci gaba a kan tsarin da take kai.
Ya bayyana hakane a ganwar da aka yi dashi kan bashin da ake bin Najeriya ta kafar sadarwar Zamani.
Yace tsarin Tattalin Arzikin Najeriya yana amfanar Masu madafan Ikone kawai yayin da talaka ke cikin wahala.
Yace tabbas yana goyon bayan a yafewa Najeriya bashin dake kanta amma itama kasar sai ta nuna cewa da gaske take wajan ci gaban al’ummarta. Yace sharadin yafe bashi shine sai an rika ayyuka na ci gaban jama’a da kudi ba wai kashesu wajan aikin yau da kullun ba. Yace dole a samar da masana’antu, a inganta Ilimi, Kamar yanda, hutudole.com ya samo muku daga THISDAY
Kamar yadda jaridar mikiya ya kuma ce dole a kula da yanda mutane ke kara yawa amma kuma Tattalin Arzikin Najeriya baya kara yawa. Yace a Najeriya ana samun mace daya ta haifi ‘ya’ya sama da 8 a wani lokacin ma yakan fi haka yawa, musamman ga masu auren mata fiye da daya.
Yace dolene sai an dauki matakin kula da hakan kamin a samu ci gaba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button