AddiniLabarai

Wane Laifi Isa Ali Pantami ya yi wa Ƴan Boƙo Aƙida ne? ~ Sheikh Aliyu Muhd Sani

Da ma tun tuni Ƴan Boko Aƙida suna matuƙar baƙin ciki da kasancewar Dr. Isa Ali Pantami a matsayin Minister, suna ta neman hanyar da za su kawar da shi daga matsayin ido rufe. Kwatsam, sai ga masoyansu Arna sun fito suna yi masa sharri, don ganin an sauke shi daga matsayinsa, sai su kuma Ƴan Boko Aƙida suka fito gadan – gadan suna taya su yaƙarsa.
To wai wane laifi ne Isa Ali ya yi wa Ƴan Boƙo Aƙida?
Babu wani laifin da ya yi musu face laifi guda ɗaya tak, shi ne; kasancewarsa Malamin Addinin Muslunci, kuma Bawahabiye.
Su abin da suke so shi ne; kar Malamin Addinin Muslunci ya zama Minister, saboda a wajensu matsayin Minister da sauran manyan muƙaman siyasa ba na Malamin Addinin Muslunci ba ne, a’a, na Arna ne, ko da kuwa Arnen Pastor ne, ko kuma Musulmin da bai damu da Addinin Muslunci ba.
Kuma ko da an yi rashin sa’a an naɗa Malami a matsayin Minister to kar a kuskura a naɗa Bawahabiye.
Wannan shi ne maƙasudin Ƴan Boko Aƙida wajen goyon bayan Arna a kan Minister Dr. Pantami.
Su a wajensu, kowa yana da haƙƙi, kuma a shirye suke su kare masa haƙƙin, su nema masa ƴanci, amma ban da Malamin Addinin Muslunci, musamman Bawahabiye. Wannan shi ne ma’anar humanity a wajensu. Ma’ana; kowa yana da haƙƙi da ƴanci, amma ban da mai nuna kishin Addinin Muslunci, shi kam ba shi da wani haƙƙi ko ƴanci.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button