Sautin Murya : Yadda Wayar Abduljabar kabara Sa Dr Abdallah G/Kaya Akan Muƙabala ta kaya Rigima sabuwa


A cikin wannan wayar tarho zaku sha dariya sosai domin Kunsan sheikh Abdallah bashi da dama ga duk wanda bai martaba fiyayyen halitta da kuma sahabbansa..
A facebook nayi karo da wani inda abun yayi bashi dariya akan wayar ga abinda ya wallafa.
“Wayar ta Mal. Abduljabbar Kabara ya yi wa Dr. Abdallah Usman Gadon Kaya ta ba ni dariya, musamman ma daga ƙarshen. Abduljabbar ya tambaye shi lambar Sheikh Qaribullah Nasiru Kabara. Dr Abdallah yace itama ba ka da ita? Haba Malam, kada ka zo mana da wasa. Wai zai nemi lambar da wani wurin.
Na so an yi zaman nan dai an wuce wajen, musamman kafin Ramadan. Amma dai, Allah ya sa jinkirin alheri ne ga Musulunci da Musulmi, amin.
Zan ajiye link na hirar a comment section ga mai son sauraro.”.
To kaima nasan zaka sha dariya akan wasu tambayoyin Abduljabar amma ga shi nan kasa sai ku saurara ga masu bukata download shima mun sanya muku.
https://youtu.be/PqZK0ZzrNho



kai allah ya mnaa me kyau amaimakon akara kokari wajan yada addin musulunci a inda be je ba, se ake tazaman muqabala kuma tsmw