Kannywood

Rarara: Fim ɗi na, ‘Gidan Dambe’, zai agaza wa ‘yan wasan Ibro

A KARON farko tun bayan rasuwar fitaccen jarumi Rabilu Musa Ɗanlasan (Ibro), shahararren mawaƙin siyasar nan, wato Dauda Adamu Kahutu (Rarara), ya ɗauki alwashin shirya wani ƙayataccen fim wanda zai dawo da martabar tsofaffin ‘yan wasan barkwanci waɗanda aka daɗe ba a ji ɗuriyar su ba a masana’antar Kannywood.
Rarara, wanda shi ne shugaban kamfanin Rarara Multimedia, Kano, ya bayyana haka a yayin da ya ke zantawa da mujallar Fim kan dalilin da ya sa zai shirya wannan fim. A tattaunawar, ya ce hakan da zai kasance wani tagomashi ne ga tsofaffin ‘yan wasan waɗanda al’umma sun fara mantawa da irin gudunmawar da su ka bayar a lokacin da tauraruwar su ta ke haskawa a ƙasar Hausa. 
Shin ko wannan fim, wanda za a fara ɗaukar sa a Kano kwanan nan, ya na a matsayin wani abu da mutane za su gani don tunawa da Ibro? Wannan tambaya ce da idan mai karatu ya biyo mu zai ji amsar ta. Bismillah:
FIM: Mai karatu zai so jin abin da ya ja hankalin ka wajen tattara waɗannan tsofaffin jaruman domin yi masu wannan aiki.
RARARA: Kamar yadda kowa ya sani, wannan ai sana’a ce kuma mu na cikin hidimar ko in ce da mu ake yin ta, kuma ko da yaushe shi ɗan kallo ya na so ya ga wani abu sabo. To waɗannan mutanen, kamar yadda aka sani, sanannu ne amma yanzu idan ka ɗauko yaro mai ƙananan shekaru wanda ba su wuce 16 ba, wani in ka tambaye shi bai ma san wa ake kira da Barmo ba ko Ɓawo, ba su san su Daɓalo ba. Kuma mutane ne waɗanda su ke nishaɗantar da mutane, su ke faɗakarwa daidai da al’adun mu da addinin mu, wanda da wuya ka ga sun tsallake wannan iyakar sun faɗa wata al’adar da ba ta dace da addinin mu ba ko wani abu.
Sannan duk abin da su ke nunawa shi ne na a ƙyale maras kyau a ɗauki mai kyau wanda kuma a hausance mutum ne ake so a nuna masa ba wai sai an yi dogon abu ba kafin a nishaɗantu ba; da barkwanci za su nishaɗantar da kai.
To gaskiya abin da ya ba ni sha’awa shi ne na ce to waɗannan mutanen bari in jawo su a jiki domin kuwa bai kamata a ce mun bar irin waɗannan mutane da su ka ba mu gudunmawa tun kafin a haife mu ko kuma tun kafin mu girma su ke bada gudunmawa kuma ga su nan mun zo mun same su da ran su, mu na kuma da damar da za mu iya yin wani abu wanda ‘ya‘yan mu idan su ka kalle su su ka ga irin gudunmawar da su ke bayarwa su amfana da hakan. Ka ga kuwa bai kamata a ce mun ƙyale su a haka ba. Shi ya sa na ce bari in yi wani abu, kuma abin mu yi shi yadda zai ɗore in Allah ya yarda.
FIM: Wane irin fim za ka shirya wa  jaruman?
RARARA: E to, duba da irin yadda ita kan ta masana’antar ta Kannywood ta canza akala, zan yi musu fim ɗin da za su daɗe su na amfana da shi, wato fim mai dogon zango, ‘series’ a turance kenan. Kuma mun yi wa fim ɗin suna wato ‘Gidan Dambe’. Kuma kasuwanci ne wanda za mu shiga, kowa ya zo ya yi aiki a biya shi.
FIM: Me ya sa ku ka zaɓi wannan labari na ‘Gidan Dambe’ a matsayin wanda za a yi fim a kan sa?
RARARA: Dalilin da ya sa mu ka ɗauki labarin na ‘Gidan Dambe’ shi ne shi wannan gida ya haɗa abubuwa da yawa, misali su kan su masu damben, shuwagabannin gidan, masu saida abinci, masu gasa nama, ‘yan kallo da dai sauran su. To ka ga kuwa dole kowa ya kasance a cikin gidan, kuma wannan shi ya ba mu sha’awa da mu dawo da su ta wannan sigar, su cigaba da faɗakar da mu iya inda za su iya. Gidan dambe gida ne wanda ya ke tattare da mutane da dama, ta haka kuma za mu samu damar kirawo jaruman da dama.
FIM: Ka na ganin haɗa waɗannan tsofaffin jaruman, musamman waɗanda su ka yi aiki da marigayi Rabilu Musa Ibro  ba zai zama abin magana ba, duba da ɓangare ɗaya ka zaɓa kuma ka ke son fifitawa?
RARARA: To ai wannan magana da ka faɗa ta marigayi Ibro, Allah ya jiƙan sa ya gafarta masa, kowa dai ya san idan aka ce Ibro an san irin finafinan da ya ke yi; finafinai ne na bada nishaɗi da kuma faɗakarwa, saboda idan za a faɗakar da kai a nishaɗance mutum ya na dariya ya na murna har ta kai an isar ma da wani saƙo a ciki na daidai da kuma wanda ba daidai ba.
Kamar dai lokacin da Ibro ya na raye shi ne a matsayin shugaban waɗannan mutane, kuma baya tun a can da ni da shi na ke mu’amala ba da su ba, na fi yin alaƙa da shi fiye da sauran da su ke tare da shi.
Bayan  da mu ka samu wannan babban rashi ba mu ƙara hoɓɓasa mun yi wani abu ba; duk da akwai jagororin, amma an samu kusan wasu sun yi nan wasu sun yi nan, to ni Allah ya yi ni ina da sha’awar wasan Rabilu kuma akwai abokan aikin su da yawa da na ke son in ga fim ɗin su tare, sai kuma da ya tafi aka rasa waɗanda za su dinga kirawo su don a sa su a fim, da man yawanci ana kiran su ne saboda shi; idan aka je aka nemo Rabilu sai a ce ai ya fi yin aiki da wane, sai ka ga an kira mutum ta dalilin sa. Kuma a cikin waɗannan ‘yan wasa da za a yi wannan fim da su har da ɗan gidan marigayi Ibro.

Dauda Adamu Kahutu (Rarara) tare da marubucin labarin diramar ‘Gidan Dambe’, Maje Elhajeej Hotoro

FIM: Jarumai nawa wannan fim ya ƙunsa?
RARARA: Tab! A gaskiya dai wannan fim ba zan iya cewa ga adadin mutanen da zai ƙunsa ba, saboda abu ne da za a fara shi yanzu kuma zai ci gaba, ba a san lokacin da aikin zai tsaya ba. Ka ga kuwa ba za a iya cewa ga adadin mutanen da ake da buƙata ba. Amma dai zuwa yanzu mun kira aƙalla mutane sama da 20 zuwa 30 waɗanda za mu fara da su.
FIM: A wace kafa za ana nuna wannan fim ɗin?
RARARA: Za mu sa shi a kan kafar nan ta YouTube, wala’alla kuma idan gidan wani TV ya nemi mu sayar masa za mu sayar musu. Idan kuma mun samu inda za mu je mu haska a sinima za mu haska. Amma dai ko ma menene, za mu dinga sawa a kafa ta YouTube.
FIM: A ƙarshe, da me za ka ƙarƙare mana da shi?
RARARA: To wannan abu dai da na yi, na yi shi ne domin taimaka wa juna. Da mutum ya zo gun ka ya ce ka ba shi, gobe ya zo ka ba shi, shi ya sa na ce to bari in zo mu yi wannan kasuwancin ta yadda kowa zai amfana.
Kuma ina sa ran cewa wannan fim ɗin zai ja ana kiran su wasu ayyukan, duk da cewa ko da mutum ya ce ka ba shi kuma mu na bayarwa, ba kowane mutum ne abin da ka ke bayarwa ba zai samu, amma ta wannan hanyar ina ganin kowa zai iya amfana da juna.
Sannan ina kira ga duk waɗanda aka ba wa ragamar jagorantar wannan fim, ya kamata su tsaya su yi abin da ya dace su yi, kuma aiki na tsakani da Allah, don kowa ya ɓata ya sani, kuma haka kowa ya gyara ya sani.
Ina so kuma na yi amfani da wannan dama in gode wa ‘yan jaridu, musamman wannan mujallar Fim ɗin. Ya kamata kuma a ce su kan su waɗanda su ke cikin wannan masa’anta su ɗauki wannan abu da muhimmanci wajen bada sahihan bayanai ga irin ku wanda ta hakan ne za mu cire zargi da shakku daga zuƙatan mutane a kan wani abu da aka ce mun aikata. Akwai waɗanda da dama za a yi abubuwa na alkairi a wannan masana’anta amma ba za su buga ba ko faɗa ba, amma da zarar na sharri ne za ka ga su ne na gaba-gaba wajen bugawa, kuma wannan abin bai kamata ba. Kamata ya yi mu zama masu taimakon kan mu da kan mu, mu kuma rufa wa junan mu asiri. Don haka ina godiya.mujallar fimmagazine na wallafa wannan rubutu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button