Gwamnatin jihar Bauchi ta dakatar da wani Zindikin Malami mai suna Abubakar Idris dake garin Azare karamar hukumar Katagum jihar Bauchi
Zindikin Malamin ya fadi kalaman zagi da batanci akan Manzon Allah (SAW) a gurin tafsirin Qur’ani da yake gabatarwa ‘yan uwansa Zindikai
Gwamnatin jihar Bauchi batayi kasa a gwiwa ba, tana samun rahoto da hujja na gaskiya ta dakatar da Malamin taree da haramta yada karatunsa a kafofin watsa labarai dake fadin jihar Bauchi
Ina mutanen Kano da Gwamnatin jihar Kano? da fatan zakuyi koyi da jihar Bauchi wajen daukar matakin gaggawa akan masu taba darajar Annabi (SAW)
Allah Ka kara wa Annabi daraja, Ka sanya mu cikin cetonsa Amin Datti Assalafy ne ruwaito wannan labari.
Leave Comment Here