Kannywood

Labari Mai Firgitarwa! Yau Za Mu Kawo Muku Gawar Ummi Zee-Zee, Sakon Wani Mutum Ga ‘Yan Uwanta

… ‘Yanda sandan Kaduna sun fara bincike
…Ummi na Kano, inji hukumar tsaro
A yayin da rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kaduna ta fara bincike a daren yau kan rasuwar da ake cewa jarumar Kannywood Ummi Ibrahim (Zee-Zee) ta yi, wani mutum wanda ba a san ko waye ba ya faɗa wa iyalin ta cewa gobe za su kai gawar ta gidan su a Kano.
A daren Jiya ne dai labari ya ɓulla cewa fitacciyar jarumar ta mutu a gidan wata ƙawar ta mai suna Khairat a Kaduna.
An ga saƙo an wallafa a shafin Zee-Zee na Instagram da sunan jarumar wai ta rasu a Unguwar Sarki.
Saƙon ya ba mutane mamaki, musamman da yake daga shafin jarumar aka tura shi, wanda hakan na nuni da cewa duk wanda ya tura saƙon, to wayar Zee-Zee na hannun sa.
Binciken da mujallar Fim ta yi a daren nan ya gano cewa wani wanda ke iƙirarin sunan sa Sufeto Khalid ya faɗa wa iyalan jarumar cewa wai ya kama Khairat da mijin ta, kuma ya na tsare da su a wani ofishin ‘yan sanda a Kaduna.
Mutumin ya tabbatar wa da iyalan jarumar cewa Zee-Zee ta rasu, wai za su kai gawar ta Kano a gobe.
Sai dai Khalid ya ƙi faɗin a wane ofishin ‘yan sanda ake tsare da waɗanda aka kama, sannan ya ƙi bada lambar wayar sa ko lambar Khairat ɗin.
Ta wayar Zee-Zee ake magana da shi lokacin da aka kira wayar tata.
Khalid ya bar ƙanwar Zee-Zee, wato Hadina Ɗan-Chaina, da sauran dangin ta cikin zullumi da damuwa, ran su cike da tambayoyi.
Sun zura wa sarautar Allah ido har zuwa gobe su ga me zai biyo baya.
Da mujallar Fim ta tuntuɓi kakakin rubdunar ‘yan sanda ta Jihar Kaduna game da iƙirarin da Khalid ya yi, sai ya ce su kam wannan nagana ba ta iso gare su ba.
Kakakin, ASP Muhammad Jalige, ya ce akwai tababa kan maganar da mutumin ya yi domin ba haka ‘yan sandan gaske ke yin aikin su ba.
Ya ce in da gaskiya ne, to da nan da nan za a sanar da hedikwata domin “ba a Division ake ‘handling case’ da ya shafi kisa ko mutuwa ba.”
Duk da haka, ya bada tabbacin cewa rundunar ‘yan sandan za ta binciki al’amarin domin gano bakin zaren, kuma duk abin da ta gano za ta sanar ba tare da ɓata lokaci ba.
A wani ɓangaren kuma, mujallar Fim ta tuntuɓi wata hukumar tsaro a Kaduna don jin abin da hukumar ta sani game da wannan al’amari.
Hukumar ta karɓi lambar wayar Zee-Zee a wajen wakilin mu, ta ce za ta bincika ta gani idan jarumar na cikin Jihar Kaduna.
Bayan wani ɗan lokaci sai hukumar ta sanar da wakilin mu cewar binciken su ya nuna masu cewar wayar Zee-Zee ba ta cikin Jihar Kaduna, ta na can cikin Sabon Garin Kano.
Ba mu ce mai wayar na da rai ko ba ta da rai ba, amma dai wayar ta ba ta cikin Jihar Kaduna,” inji hukumar.
Madogara: Fim Magazine

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button