Labarai

Kullum Jibga ta yake amma na Kasa Rabuwa da shi saboda Kudi: Cewar Budurwa

Matashiyar ta ce sun fara soyayya ne kimanin watanni takwas da suka gabata, kuma lashakka soyayya ta yi dadi domin babu irin kudin da ba ya kashe mata, sai dai kash ya maida ta tamkar yar shi saboda musgunawa.
Wata Matashiya a Najeriya ta bayyana irin halin lahaula da ta shiga sakamakon irin yadda daular duniya ta rude ta.
kamar yadda Jaridar demokuradiya na ruwaito.Matashiyar da ta bukaci a sakate sunan ta, ta ce ta shiga wani halin rayuwa sakamakon irin hibga da saurayin ta ke mata tamkar yar shi ta cikinsa.
Matashiyar ta ce sun fara soyayya ne kimanin watanni takwas da suka gabata, kuma lashakka soyayya ta yi dadi domin babu irin kudin da ba ya kashe mata, sai dai kash ya maida ta tamkar yar shi saboda musgunawa.
Ta ce babu abinda ta nema a gurin shi ta rasa domin yana da kudi na fili da na boye, a don haka ne ta ji babu wani sai duk da cewa a fadin ta ba don Allah take son shi sai dai don gina kanta daga bisa ta kama gabanta.
Kamar yadda ta fadi a yanzu tana shirin tatsar shi ne ta yi gaba don kama wani kasuwanci da za ta dogara da kanta don samun suk irin miji da take so.
“Don Allah Jama’a a taimaka mun da shawara, babu matsala ko da za a yi dariya ta, amma dole na fadi abinda ke taba mini Zuciya”
“Ina da saurayi kuma yana da kudi sosai, idan da wanda ta taɓa shiga hali irin nawa ta taimaka mun da mafita, sabida kullum jibga ta yake babu kakkautawa”
“Buri na yanzu shine na samu hanyar da zan tatse shi na yi gaba kawai amma na kasa, mecece shawarar Ku?
Ko da yake matashiyar kawo yanzu ba ta bayyana kan ta ba, amma bisa ga dukkan alamu irin yan matan nan ne dake burin gina rayuwa a kan karya, kuma an ce duk wanda yaƙi jin bari, to lallai zai ji hoho.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button