Labarai

Jami’an tsaro sun hallaka kwamandan IPOB (Hotuna

Advertisment

)
Hadakar jami’an rundunar ‘yan sanda ta Najeriya da takwarorinsu na Sojojin Najeriya da kuma na Hukumar Tsaro ta SSS, a wani samamen hadin gwiwa, da sanyin safiyar ranar Asabar sun mamaye hedikwatar ‘yan kungiyar IPOB da ke kauyen Awomama na karamar hukumar Oru ta Gabas ta Jihar Imo, inda suka kashe da ‘yan yan tawayen da dama ciki har da babban kwamandan masu tayar da kayar baya a yankin Kudu Maso Gabas wanda aka fi sani da Ikonso.
‘Yan tawayen ne dai ke da alhakin harin da aka kaiwa Hedikwatar ‘yan sanda ta jihar Imo da kuma hedkwatar Hukumar Kula da Fursunoni ta Nijeriya a ranar 5 ga Afrilu, 2021.
Sun kuma kai wasu munanan hare-hare kan jami’an tsaro da kuma cibiyoyi a kudu maso gabas da kudu maso kudancin kasar.
Kwamanda Ikonso an san shi da sunan Mataimakin Shugaban kasa da kuma mai kula da dukkan ayyukan mayakan kungiyar. Shi ne mai tsarawa da kuma jagorantar harin da aka kaiwa Hedikwatar ‘yan sanda ta Imo da wasu hare-hare da dama kan jami’an tsaro da sojoji.
Bayan artabun da aka gwabza, rundunar tsaron ta gano gawar Kwamanda Ikonso da mayakansa guda shida (6).
An kuma kwato manyan makamai da dama ciki har da bindigogin AK47 guda shida, da daruruwan harsasai daban-daban da kuma layu da dama daga hannun maharan.
‘Yan sanda uku da jami’in soja daya na karbar kulawa, bayan sun samu munanan raunuka a yayin musayar wuta da maharan.
#OakTVHausa

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button