Labarai

Bamu dakatar da Kwankwaso ba – Uwar jam’iyyar PDP

Jam’iyyar PDP ta ƙasa ta yi watsi da wani labari da ake yaɗawa, na cewa ta kori tsohon Gwamnan Kano Rabi’u Kwankwaso daga jam’iyyar.
Kamar yadda Freedomradio na ruwaito Hakan na cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa Kola Ologbondiyan ya fitar da yammacin Lahadi.
Sanarwar ta bayyana ƙarara cewa, labarin da ake yaɗawa labari ne na ƙanzon kurege, a don haka ba ta dakatar da Kwankwaso ba.
Jam’iyyar ta jaddada cewa, kundin tsarin mulkin ta ya tanadi matakan da ake bi domin dakatar da mamba a kwamitin zartarwa na ƙasa ba wai kara-zube ba.
Ologbondiyan ya ƙalubalanci masu yaɗa labarin kan su kawo matakan da aka bi domin zartar da wannan mataki.
Jam’iyyar ta PDP ta kuma gargaɗi masu yaɗa wannan labarin da cewa ba zata lamunci hakan ba, domin zai iya taɓa ƙima da mutuncin jam’iyyar.
A wani ci gaban labarin kuma jam’iyyar ta PDP ta ƙaryata labarin cewa ta dakatar da tsohon Gwamnan jihar Neja Babangida Aliyu.
Jam’iyyar ta ce, ta lura da wani labari mara tushe da ake yaɗawa na cewar ta dakatar da shi.
A ƙarshe PDP ta nemi shugabanni da mambobin ta kan su yi watsi da irin waɗannan labarai, su haɗa kan su domin ciyar da jam’iyyar gaba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button