An kama wasu mutane a makabarta da ƙoƙon kan mutum a Kaduna


Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta ce, ta kama wasu mutane biyu wadanda ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne da ƙoƙon kan mutum.
Kakakin rundunar ASP Muhammad Jalige ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.
Kamar yadda BBCHAUSA na ruwaito Jalige ya ce a ranar Juma’a ne da misalin 11 na dare aka sanar da su cewa an ga wasu mutane a wata makabarta da ke yankin Kudenden kuma ana zargin wani mugun abu suke aikata wa.
“Da samun wannan rahoto ne jami’anmu suka bazama kuma suka yi nasarar kama mutane biyu da suka fito daga yankin Kabala a jihar.
“Garin bincike an gano shebir a tare da su da kuma ƙoƙon kan mutane,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Kakakin ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike a kan mutanen kuma da zarar an kammala za a gurfanar da su gaban kuliya