An ceto yarinyar da iyayenta suka kulle tsawon shekaru 10 a Kano (Hotuna)
An ceto yarinya ƴar shekara 15 da iyayenta suka ɗaure tsawon shekara 10 a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Rundunar ƴan sandan jihar ne suka ceto yarinyar a ranar Litinin mai suna Aisha Jubril.
An kulle yarinyar ne a ɗaki tun tana ƴar shekara biyar.
Rundunar ƴan sandan Kano ta ce ta samu rahoto game da yarinyar misalin ƙarfe 11 na safe, kuma nan take Kwamishinan ƴan sandan jihar ya bayar da umarnin a gaggauta ceto yarinyar.
Kamar yadda BBCHAUSA na ruwaito.Ƴan sandan sun ce sun samu yarinyar cikin wani mawuyacin hali na tsananin yunwa da kuma buƙatar kula da lafiyarta saboda irin yanayin da suka samu wurin da aka kulle ta.
Yanzu haka yarinyar ana diba lafiyarta a asibitin Murtala a Kano.
Ƴan sandan kuma sun cafke mahaifiyarta mai shekara 35 da ake kira Rabi Mohammed yayin da mahaifinta kuma ya tsere a cewwar rundunar ƴan sandan ta Kano.
A bara an ta samun irin wannan al’amari a Kano da sauran jihohin arewacin Najeriya inda ake kullewa ko ɗaure yara ƙanana.
Saɓanin yadda yawanci kishiyoyi ke aikata wannan aikin, amma wannan asalin iyayenta ne ake zargi sun kulle ta.
Ƴan sanda sun ce suna gudanar da bincike, idan sun kammala za su tura waɗanda ake zargi kotu.