Labarai

‘Ƴan siyasar Najeriya sun mallaki dukiyar dala miliyan 400 a London da Dubai’

Advertisment

Wani jami’i a cibiyar nazari ta Chatham House da ke Burtaniya Matthew Page,ya shawarci masu bincike su maida hankali kan harkokin gine-gine da bangaren ilimi idan suna bibiyar batun almundahana da zirarar kudade ta hanyoyin da ba su dace ba.

Ya ba da wannan shawarar ce a wani taron karawa juna sani da aka shirya wa masu bincike da ke bibiyar hada-hadar haramtattun kudade.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ICPC ce ta shirya taron inda aka zabo mahalarta daga sauran hukumomi masu tabbatar da doka.

Jaridar bbchausa ta rawaito Mista Page na jaddada bukatar a sa ido kan bangarorin biyu – harkar gine-gine da ilimi saboda suna bai wa yan siyasa damar yin sama da fadi da kudade.

Advertisment

“Akasarin dukiyoyin da yan siyasar Najeriya ke mallaka a London da Dubai na hannun wasu makusanta ko iyalai ko kamfanonin mai na Shell”.

“Sama da gidaje dala miliyan 400 ake dangantawa da yan siyasa.” in ji Mista Page.

Article share tools

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button