Yar Kano ce ta lashe Musabakar al-Kur’ani ta kasa bangaren mata
Yar Kano ce ta lashe musabakar kur'ani ta mata dan Zamfara ya lashe ta maza
A yau ne aka kammala musabakar Al-kur’ani mai girma ta kasa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya.
An fara musabakar ne kwanaki takwas baya, inda a yau kwana na tara aka kammala ta.
Muhammad Auwal Gusau shi ne gwarzon musabakar ta bana bangaren maza, kuma ya fito ne daga jihar Zamfara.
Kamar yadda Bbchausa na ruwaito.Ya kara da masu karatu da yawa in da a karshe ya samu nasara a matakin karatun izu 60 da tafsiri.
Sai Nusaiba Shuaibu Ahmad daga bangaren mata, wadda ita ma ta zo ta daya a bangaren izu 60, kuma yar asalin jihar Kano ce.
A yayin bikin an nadawa Muhammad Auwal Gusau rawani, cewa ya zama kangaran kuma zakaran gwajin dafi a tsakanin gwanayen al-Kur’ani mai girma.
Man yan makaranta ne suka halarci taron daga sassa daban-daban na Najeriya.
Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya halarci wurin rufe wannan gasa ta karatun al-Kurani.
Haka kuma mafi yawan wadanda ba su samu nasara ba tun daga matakin farko na gasar har zuwa karshe sun halarci taron rufe gasar.